AFCON 2025: Wasu Fitattun 'Yan Wasan Najeriya 4 na Fuskantar Dakatarwa
Morocco - Yayin da tawagar Super Eagles ke shirin buga wasan ƙarshe na rukunin C da Uganda a gasar cin kofin nahiyar Afrika ta 2025, Najeriya ta riga ta samu tikitin zuwa zagayen 'yan 16.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Sai dai duk da wannan nasara ta farko, ƙalubalen da ke gaban Najeriya yanzu ba batun cancanta ba ne, sai dai batun 'yan wasa hudu da ke fuskantar dakatarwa kafin fara wasannin 'kifa daya kwala'.

Source: Getty Images
Tarihin AFCON ya nuna cewa sau da dama ƙungiyoyi na shan kaye ne ba wai don rashin ƙwarewa ba, sai dai don rasa manyan ‘yan wasa saboda tarin katinan gargadi da aka ba su, in ji rahoton Premium Times.
A halin yanzu, akwai ‘yan wasa huɗu masu matuƙar muhimmanci a Super Eagles da ke tafiya kan siradi, domin kowannensu na da katin gargadi.
Idan wadannan 'yan wasan da suka kuskura suka samu kati, to kuwa za su fuskanci dakatarwa daga buga wasa a zagaye na gaba.
Barazanar dokokin hukumar CAF
Dokokin Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afrika (CAF) sun tanadi cewa ba a gogewa dan wasa katunan gargadi da aka ba shi har sai an shiga zagayen 'kifa daya kwala'.
Wannan na nufin cewa duk ɗan wasa, daga cikin 'yan wasan Najeriya hudu da ya sake samu katin gargadi a wasan Uganda, zai rasa wasan zagaye na 16.
Wannan doka ta sanya koci Eric Chelle da tawagarsa cikin tsananin tunani kan yadda za su tafiyar da wasan da Uganda, musamman ganin cewa wasan ba shi da tasiri kai tsaye kan cancantar Najeriya.
'Yan wasan Najeriya da ke fuskantar dakatarwa
1. Semi Ajayi

Source: Getty Images
Ɗan wasan baya Semi Ajayi ya kasance ginshiƙi wajen tsaron Najeriya, musamman a tare kwallon da aka harbo su kai tsaye, da na sama da kuma sauya tsari daga tsaro zuwa kai hari.
Rashinsa a zagayen 'kifa daya kwala' zai zama babbar barazana ga Najeriya, domin haɗin kai da fahimtar juna a tsaron baya abu ne mai matuƙar muhimmanci.
Idan aka dakatar da Ajayi, hakan na iya tilasta wa koci yin babban sauyi a tsaron baya, inda ake ganin Igoh Ogbu na iya samun damar dawowa tsakiyar baya, duk da cewa bai buga wasa ba tun bayan wasan sada zumunci da Masar kafin fara gasar.
2. Stanley Nwabali

Source: Getty Images
Mai tsaron raga Stanley Nwabali ya fuskanci kalubale a wasu lokuta a wannan gasar, musamman a wasan da ya gabata. Bayan batun ƙwarewa, batun yadda zai kama kansa yanzu ake yi.
Ajiye shi a benci a wasan Uganda na iya zama dabara mai ma’ana, domin hakan zai kare shi daga dakatarwa tare da ba shi damar sake samun nutsuwa kafin fara wasannin 'kifa daya kwala'.
A irin wannan yanayi, Francis Uzoho na iya samun damar tsare ragar Najeriya, wanda dama bai shiga fili ba a wasanni biyu da Najeriya ta buga.
A gasa irin AFCON, rashin tabbas a raga na iya zama sanadin faduwar ƙungiya, don haka dole ne a kula da wannan bangare sosai.
3. Victor Osimhen

Source: Getty Images
Victor Osimhen shi ne jigon harin Super Eagles. Gudunsa, ƙarfin faɗa da iya cin kwallo sun sanya shi zama babbar barazana ga kowace ƙungiya.
Amma duk da haka, kuskure ɗaya kacal, ko katin gargadi sakamakon tashin hankali, na iya hana shi buga zagayen gaba, in ji rahoton Vanguard.
Tunda an riga an samu gurbin tsallakewa, masu ruwa da tsaki na ganin ya dace a hutar da Osimhen domin kare shi daga duk wata barazana. Paul Onuachu na da damar maye gurbinsa, inda zai kawo salo daban na kai hari, musamman a buga kwallo ta sama.
Hutar da Osimhen ba rauni ba ne a irin wannan lokaci, illa ma nuna cewa Najeriya na tunanin lashe kofi, ba kawai nasarar rukuni ba.
4. Ademola Lookman

Source: Getty Images
Ademola Lookman ya kasance ɗaya daga cikin fitattun ‘yan wasa a AFCON 2025 zuwa yanzu. Ya zura kwallo a wasanni biyu, tare da nuna kuzari, saurin gudu da ƙwarewa a gaba.
Sai dai wannan tasiri nasa ya sa dakatarwarsa za ta zama babban rashi. Don haka, gyara salon wasansa a wasan Uganda ya zama tilas.
Idan aka ajiye Ademola Lookman a benci kuma, hakan zai iya bai wa Samuel Chukwueze damar komawa cikin ‘yan wasan farko, musamman bayan sauye-sauyen dabara da aka gani a wasan baya inda aka ƙara ƙarfin tsakiya da shigar Frank Onyeka.
Babban hangen nesa na gasar AFCON 2025
A zahiri, wasan Uganda ba shi ne babban abin dubawa ba. Abin da ke gaba shi ne zagayen 'kifa daya kwala', inda kuskure guda ɗaya zai iya kawar da ƙungiya daga gasar.
Osimhen, Lookman, Ajayi da Nwabali su na daga cikin manyan 'yan wasan Super Eagles. Yadda za a kula da su a yanzu zai iya zama mabuɗin nasarar Najeriya ko kuma dalilin nadamar da za a yi daga baya.
Jaridar Punch ta rahoto cewa a gasar AFCON, ba fasaha kaɗai ke lashe kofi ba — lokaci, ladabi, tsari da haƙuri su ne ke raba zakara da mai kallo.
'Yan kwallon Afrika da ba su daga AFCON ba
A wani labari, mun ruwaito cewa, akwai 'yan wasan kwallon kafa na Afrika da har kawo yanzu ba su taba daga kofin AFCON ba, har ma wasu daga cikinsu sun yi ritaya.
Kofin Nahiyar Afirka (AFCON) shi ne babban kofin kwallon kafa na maza a Afirka, wanda hukumar da ke kula da kwallon kafa ta Afirka (CAF) ke shirya wa.
Mohamed Salah, Didier Drogba na daga cikin 'yan wasan Afrika biyar da duk da irin kwarewarsu, da shaharar da suka yi a Turai, ba su iya daga kofin ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



