Tinubu Ya Tura Tawaga Morocco yayin da Najeriya Za Ta Fafata da Tanzania a AFCON 2025

Tinubu Ya Tura Tawaga Morocco yayin da Najeriya Za Ta Fafata da Tanzania a AFCON 2025

  • Shugaba Bola Tinubu ya aike da wata babbar tawaga zuwa Morocco domin ƙarfafa gwiwar Super Eagles gabanin wasansu da Tanzania
  • Tawagar ta ƙunshi manyan jami’an gwamnati da shugabannin wasanni, ciki har da sanatoci, ‘yan majalisa, shugabannin NFF da NSC
  • Wakilan shugaban sun miƙa kyaututtuka da karramawa da Tinubu ya yi alkawari tun bayan AFCON 2023, domin ƙarfafa ‘yan wasan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya nuna cikakken goyon bayansa ga Super Eagles, ta hanyar aika wata tawaga ta musamman zuwa kasar Morocco, inda ake gudanar da gasar cin kofin AFCON 2025.

Najeriya za ta fafata wasan ta na farko a rukunin C ne da kasar Tanzania, a filin wasa na Fez Stadium, birnin Fez, da yammacin Talata, 23 ga Disamba.

Kara karanta wannan

An saka ranar da Trump zai hana 'yan Najeriya shiga kasar Amurka

Tinubu ya tura wakilai domin karfafa gwiwar 'yan wasan Super Eagles a wasansu da Tanzania a Morocco
Shugaba Bola Tinubu da 'yan wasan kungiyar kwallon kafasr Najeriya, Super Eagles. Hoto: @officialABAT, @NGSuperEagles
Source: Getty Images

Wasan na da matuƙar muhimmanci, domin shi ne zai fara nuna yadda Super Eagles za su taka rawar gani a gasar, kamar yadda rahoton BBC ya nuna.

AFCON 2025: Tinubu ya tura wakilai Morocco

A cikin wata sanarwa da aka wallafa shafin X, dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Gusau/Tsafe a jihar Zamfara, Kabiru Amadu Mai Palace, ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya aike da manyan jami’ai domin wakiltarsa.

Tawagar ta ƙunshi:

  1. Sanata Abdul Ningi – Shugaban kwamitin wasanni na majalisar dattawa
  2. Kabiru Amadu Mai Palace – Shugaban kwamitin wasanni na majalisar wakilai
  3. CG Bashir Adewale Adeniyi – Kwanturola Janar na hukumar Kwastam ta Najeriya
  4. Shehu Dikko – Shugaban hukumar wasanni ta kasa
  5. Ibrahim Musa Gusau – Shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF)
  6. Janet Olisa – Mai ba Shugaba Tinubu shawara kan harkokin kasa da kasa
  7. Mukaddashin jakadan Najeriya a Morocco

Kara karanta wannan

Bangarori 4 da Tinubu zai fi kashewa kudi a kasafin 2026

Tinubu ya cika alkawari ga 'yan Super Eagles

Kabiru Amadu ya bayyana cewa tawagar ta ziyarci ‘yan wasan Super Eagles a sansanin horarwarsu, inda suka miƙa musu kyaututtuka da Shugaba Tinubu ya yi alkawari tun bayan da Najeriya ta zo ta biyu a AFCON 2023 da aka gudanar a Ivory Coast.

A cewarsa, kyaututtukan sun haɗa da gidaje, filaye, da karramawar ƙasa, domin ƙara musu ƙwarin gwiwa da nuna godiya ga jajircewarsu.

“Mun je mun wakilci shugaban kasa, mun kuma tabbatar da cewa dukkan alƙawuran da ya yi wa ‘yan wasan sun cika. An yi hakan ne domin ƙarfafa musu gwiwa kafin wasansu na farko,” in ji Kabiru Amadu.

Tawagar ta kuma duba yanayin jin daɗin ‘yan wasan, inda ta tabbatar da cewa babu wata matsala ta masauki, lafiya ko horarwa.

Najeriya za ta fafata da kasashe 3 a rukunin C a gasar neman cin kofin nahiyar Afrika (AFCON).
Taron tsara gasar cin kofin nahiyar Afrika (AFCON) da za a gudanar a Morocco. Hoto: @CAF_Online
Source: Getty Images

Jadawalin wasannin Najeriya a rukunin C

Najeriya za ta kara da Tanzania da yammacin Talata da ƙarfe 6:30 na yamma. Bayan haka, Super Eagles za su fuskanci Tunisia da kuma Uganda a sauran wasannin rukunin C.

Kara karanta wannan

Tsofaffin 'yan majalisa sun kawo wanda suke fatan ya zama gwamnan Kano a 2027

Masu sharhi na wasanni na ganin cewa goyon bayan shugaban kasa da wannan ziyara na iya ƙara wa ‘yan wasan kwarin gwiwa wajen neman lashe kofin da Najeriya ke fata tun shekaru da dama.

CAF ta saki jadawalin wasannin AFCON 2025

Tun da fari, mun ruwaito cewa, hukumar CAP ta saki jadawalin wasannin rukunai na gasar cin Kofin Nahiyar Afrika ta 2025 (21 ga Disamba 2025 – 18 ga Janairu 2026) a Morocco.

A yanzu kasashe 24 sun san abokan karawarsu a taron fitar da jadawalin da aka gudanar a Rabat ranar Litinin (27 ga Janairu), ciki har da Cote D'Ivoire mai rike da kofin.

Za a gudanar da gasar cikn kofin nahiyar Afrika, watau AFCON 2025 a cikin garuruwa shida a tsawon makonni huɗu, a karshe dai, ƙasa ɗaya ce za ta iya zama zakarar gasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com