Ahmed Musa Ya Kawo Karshen Bugawa Najeriya Kwallo bayan Kafa Tarihi

Ahmed Musa Ya Kawo Karshen Bugawa Najeriya Kwallo bayan Kafa Tarihi

  • Ahmed Musa ya sanar da yin ritaya daga buga kwallon kafa a matakin kasa bayan shafe shekaru 15 yana wakiltar Najeriya a tawagar manya
  • Dan wasan wanda ya kasance cikin tawagar Super Eagles da ta lashe Kofin Nahiyar Afirka (AFCON) a shekarar 2013, ya gode wa masoyansa a gida da wajen Najeriya bisa goyon bayan da suka ba shi
  • Ya kuma taba wakiltar Najeriya a kungiyoyin ’yan kasa da shekaru 20 (U20) da 23 (U23) a farkon fara taka ledarsa, tare da buga wasa a kungiyoyi da dama a kasashen waje

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Ahmed Musa ya sanar da kawo karshen buga leda a tawagar Super Eagles ta Najeriya.

Ahmed Musa wanda ya fara taka leda a tawagar Super Eagles a shekarar 2010, shi ne dan wasan da ya fi kowa yawan bugawa Najeriya wasa a matakin manya, inda ya buga wasanni 111.

Kara karanta wannan

Yadda Mikel Obi ya kira Buhari da kansa game da alawus a gasar kofin duniya

Ahmed Musa ya yi ritaya daga bugawa Super Eagles wasa
Ahmed Musa na murnar zurawa Najeriya kwallo Hoto: PHILIPPE DESMAZES
Source: Getty Images

Ahmed Musa ya sanar da hakan ne shafinsa na X a ranar Laraba, 17 ga watan Disamban 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ahmed Musa ya yi ritaya daga Super Eagles

Shahararren dan wasan ya bayyana cewa lokaci ya yi da zai yi ritaya daga bugawa Super Eagles wasa.

Ya kawo karshen gagarumar tafiyarsa ta taka leda a matakin kasa bayan ya fara daga kungiyoyin matasa kafin daga bisani ya shiga Super Eagles.

“Na fara wannan tafiya ne ina karamin yaro. Ina matashi, ina koyon abubuwa, ina yawan tafiya, amma ban taba korafi ba. Duk lokacin da Najeriya ta kira ni, ina amsawa."
“Na sanya wannan tambari da alfahari tsawon shekaru 15. Daga yaro mai shekaru 17 da ke amsa kowane kira 🇳🇬 zuwa dan wasan Super Eagles da ya fi kowa yawan bugawa kasa wasa da wasanni 111.”
“Zakaran AFCON. Dan wasan Najeriya da ya fi kowa cin kwallo a gasar cin kofin duniya. Kyaftin. Bawa. Mai imani. Na bayar da duk abin da nake da shi. Na gode Najeriya… zuciyata za ta ci gaba da bugawa don kasa ta”

Kara karanta wannan

Yadda Buhari ya yarda matarsa, Aisha za ta kashe shi a Aso Rock Villa

- Ahmed Musa

Yana cikin tawagar da ta lashe AFCON

Ahmed Musa ya kasance cikin tawagar Super Eagles da ta lashe AFCON 2013 karkashin jagorancin marigayi Stephen Keshi, kuma ya buga gasar sau hudu a rayuwarsa.

Bayan ritayar Vincent Enyeama a watan Oktoban 2015, tsohon kocin Najeriya, Sunday Oliseh, ya nada Ahmed Musa a matsayin kyaftin din tawagar.

Sai dai a shekarar 2016 an sauya wannan matsaya inda aka nada Mikel John Obi a matsayin kyaftin, Musa kuma ya koma mataimakin kyaftin.

Bayan ritayar Mikel Obi, Ahmed Musa ya dawo ya rike ragamar jagorancin tawagar.

“Kasancewa kyaftin din Super Eagles ya koya min abubuwa da dama game da daukar alhaki, hakuri da fifita wasu a kaina. Ba wai game da umarni ba ne, illa taimakon tawaga da tsayawa tsayin daka wajen kare tambarin kasa.”

- Ahmed Musa

Ahmed Musa ya yi daina bugawa Super Eagles kwallo
Ahmed Musa na murnar kwallon da ya zurawa Najeriya Hoto: PHILIPPE DESMAZES
Source: Getty Images

Wane tarihi Ahmed Musa ya kafa?

Ahmed Musa shi ne dan wasan Najeriya da ya fi kowa cin kwallo a gasar cin kofin duniya, inda ya zura kwallaye biyu a ragar Argentina a gasar 2014 a Brazil, sannan ya sake zura kwallaye biyu a ragar Iceland a gasar 2018 a Rasha.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban kasa, Gowon ya mutu? Hadiminsa ya fito da gaskiya

“Lashe AFCON 2013 zai ci gaba da zama abin tunawa na musamman. Cin kwallo a gasar cin kofin duniya, a kan Argentina da Iceland, abubuwa ne da zan rika kasancewa da su a raina har abada.”

- Ahmed Musa

Ahmed Musa ya yi godiya

Ahmed Musa ya gode wa masu horaswa, shugabanni, masoya da abokan wasansa, yana mai cewa:

“Wasan kwallo ya ba ni sana’a, amma Najeriya ta ba ni ma’ana. Yayin da nake barin wasan kasa, ina yin hakan ne cikin kwanciyar hankali da godiya."

Ahmed Musa, wanda ya fara taka leda a GBS Academy, ya taba buga wasa a kungiyoyi da dama da suka hada da Kano Pillars, CSKA Moscow, Leicester City da Al Nassr.

Ahmed Musa ya samu mukami

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ba shahararren dan wasan kwallon kafa, Ahmed Musa, mukami.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada Ahmed Musa a matsayin Manaja na kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars.

Nadin da aka yi wa Ahmed Musa na zuwa ne a lokacin da Gwamna Abba Yusuf ya kafa sabon kwamitin gudanarwa na kungiyar Kano Pillars.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng