Babu Ahmed Musa a Jerin 'Yan Wasan Najeriya 55 da Za Su Iya Buga Gasar AFCON
- Kocin Super Eagles, Eric Chelle ya fitar da jerin ƴan wasa 54 da ke da damar wakiltar Najeriya a gasar AFCON ta 2025/2026
- Jerin ya hada da ’yan wasa da ke taka leda a waje da kuma wasu daga NPFL, inda a cikinsu za a zaɓi 28 da suka fi cancanta
- Sai dai, a gaba daya jerin ƴan wasa 54 da Chelle ya fitar, ba a ga sunan tsohon kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kocin Super Eagles, Eric Chelle ya fitar da jerin ƴan wasa 54 da ke da damar wakiltar Najeriya a gasar AFCON cikin wannan wata, inda daga bisani za a zaɓi 28 da suka fi cancanta.
Sai dai, a gaba daya jerin ƴan wasa 54 da aka fitar, ba a ga sunan fitaccen dan wasan kungiyar, kuma tsohon kyaftin dinta, Ahmed Musa ba.

Source: Getty Images
An fitar da tawagar Super Eagles da za ta AFCON
Ahmed Musa ya wakilci Super Eagles sau hudu a gasar, duk da cewa bai buga ko wasa ɗaya ba a gasar ta 2023, in ji wani rahoton BBC Hausa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fitattun ’yan wasan Najeriya da suka yi fice a wasanni na duniya sun samu gurbi a cikin jerin da aka fitar a ranar Talata, 02 ga Disamba 2025.
'Yan wasan da suka shiga jerin sun hada da kyaftin William Troost-Ekong, Victor Osimhen, Wilfred Ndidi, Stanley Nwabali da Maduka Okoye.
Sauran sun hada da Calvin Bassey, Zaidu Sanusi, Semi Ajayi, Frank Onyeka, Alex Iwobi, Raphael Onyedika, Ademola Lookman, Simon Moses, Samuel Chukwueze da Chidera Ejuke.
AFCON: Chelle ya bai wa ’yan NPFL dama
Kocin ya kuma fadada binciken sa ta hanyar kiran ’yan wasan cikin gida irin su Abdulrasheed Shehu, Ebenezer Harcourt, Ekeson Okorie, Chisom Orji da Adekunle Adeleke.
Wannan mataki ya fayyace cewa yana son ganin kwarewar 'yan wasan da ke buga wasannin kofin NPFL, da kuma tantance kwarewarsu kafin ya kammala zabin karshe na ’yan wasa 28.
Shi ma Musa wanda ya taka leda a Turai yanzu yana buga wasa ne a kungiyar Kano Pillars.
Super Eagles za su bude sansanin atisaye a Masar ranar 10 ga Disamba, 2025 inda za su buga wasannin gwaji, a cewar rahoton Channels TV.

Source: Getty Images
Super Eagles da jadawalin AFCON 2025
Jerin da aka fitar ya kunshi masu tsaron gida shida, masu tsaron baya 13, ’yan wasan tsakiya wasa 12, sannan kuma akwai 'yan wasan gaba 23.
Ebenezer Akinsanmiro na Inter Milan, wanda yake wasa a Pisa yanzu, ya samu gurbi a jerin wucin-gadi, kuma ana sa ran zai shiga jerin karshe.
Najeriya za ta fitar da jerin ’yan wasa 28 a ranar 11 ga Disamba, 2025 ko kafin wannan lokaci, domin za a fara buga wasan AFCON din ne daga 21 ga Disamba 2025 zuwa 18 ga Janairu 2026.
Super Eagles za su fafata da Tanzania, Uganda da Tunisia a rukuni na C, a cewar rahotannin da aka samu.
Ahmed Musa ya raba motoci a Kano Pillars?
A wani labarin, mun ruwaito cewa, dan wasan Super Eagles, Ahmed Musa, ya yi martani kan rahoton cewa ya raba motoci ga yan Kano Pillars.
Ahmed Musa ya karyata rade-radin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ya bai wa ’yan wasan Kano Pillars da jami’ai motoci masu tsada.
Soshiyal midiya ta kaure da labarin cewa Musa ya bai wa kowane ɗan wasa da jami’in koyarwa sababbin motoci kirar 'Land Cruiser' domin bikin dawowarsa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


