Ahmed Musa Ya Nuna Damuwa bayan Tayar da Tarzoma a Wasan Kano Pillars
- Shugaban kula da kungiyar Kano Pillars, Ahmed Musa, ya nemi afuwa bisa tashin hankalin da ya auku a Kano
- Ahmed Musa ya bayyana abin da ya faru a matsayin abin takaici da kunya da bai dace da darajar kwallon kafa ba
- Ya sha alwashin hada kai da hukumomi don hukunta wadanda suka tada rikicin da bata sunan Kano Pillars
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Shugaban Kano Pillars, Ahmed Musa, ya nemi afuwa kan tashin hankalin da ya faru bayan wasan kungiyar da Shooting Stars ta Ibadan a filin wasan Sani Abacha.
Rahotanni sun bayyana cewa an samu tashin hankali ne a filin wasan a ranar Lahadi, 12, Oktoba, 2025.

Source: Facebook
Musa, wanda tsohon kyaftin ne na Super Eagles, ya bayyana tarzomar da magoya bayan Pillars suka tayar a matsayin abin kunya da rashin kwarewa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan
An gano tsofaffin shugabannin Najeriya 3 da ba su halarci taron majalisar koli ba
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ahmed Musa ya ba da hakuri ga ‘yan wasan 3SC, masu horarwa da magoya bayan da suka shaida abin da ya faru.
Ahmed Musa ya ba da hakuri
A sokon da ya fitar, Ahmed Musa ya ce kwallon kafa wasa ne na hadin kai da farin ciki, ba na tashin hankali ba.
Leadership ta wallafa cewa ya ce:
“Tashin hankali ba abin yi ba ne a kwallon kafa, kuma abin Allah wadai ne.”
Ya bayyana cewa an kirkiro kwallon kafa ne don kawo farin ciki da zumunci, don haka duk lokacin da ta rikide zuwa tashin hankali, wajibi ne a dauki mataki, ba wai a yi shiru ba.
Ahmed Musa ya kara da cewa Kano Pillars za ta hada kai da hukumomin tsaro da na gasar NPFL don gano wadanda suka hada baki wajen kai hari ga ‘yan wasan Shooting Stars da jami’an wasa.

Source: Getty Images
Kano Pillars za ta dauki mataki
Ahmed Musa ya ce kulob din ba za ta tsaya da neman afuwa kawai ba, domin ya san kalmar afuwa ba za ta wadatar ba.
“Zamu dauki mataki mai karfi a cikin gida don tabbatar da irin wannan abin ba zai sake faruwa ba,”
- In ji shi.
Ya yi kira ga magoya bayan Pillars da su rika nuna kaunarsu ta hanyar lumana da biyayya, yana mai cewa goyon baya na bayyana ne da nuna ladabi da girmamawa, ba tashin hankali ba.
Kano Pillars na son dawo da martabarta
Ahmed Musa ya jaddada cewa kungiyar Kano Pillars za ta ci gaba da kokarin dawo da martaba da girmanta a idon duniya.
Ya ce:
“Ga NPFL, ga Shooting Stars, ga jami’an wasa, da duk masu son kwallon kafa a Najeriya — muna neman afuwa. Ni kaina na nemi afuwa.”
Bayanin Ahmed Musa ya zo ne bayan magoya bayan Pillars sun mamaye fili a lokacin da Shooting Stars ta zura kwallo a minti na 94, lamarin da ya janyo rikici kuma aka tashi da ci 1:1 a wasan.
'Yan wasan Kano sun rasu a hadari
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Barau Jibrin ya yi kyauta ta musamman ga iyalan 'yan wasan Kano da suka rasu.
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan wasan sun rasu ne bayan wani mummunan hadarin mota da ya rutsa da su.
Yayin ziyarar da ya kai ga iyalan da suka rasa 'yan uwansu, Sanata Barau Jibrin ya ba su kyautar jimillar kudi N22m.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

