'Ku Taimaka Ku Zo': Gwamna Zai Raba Tikiti Kyauta domin Kallon Wasan Super Eagles

'Ku Taimaka Ku Zo': Gwamna Zai Raba Tikiti Kyauta domin Kallon Wasan Super Eagles

  • Gwamnatin Akwa Ibom ta sayi tikitin wasan Super Eagles da Zimbabwe, za a raba kyauta ga magoya baya a filin wasa na Uyo a yau Talata
  • Super Eagles na bukatar nasara bayan rashin katabus a wasanni hudu na farko, ciki har da canjaras 1-1 da Zimbabwe a watan Nuwambar 2023
  • Kyauta za a raba a tashoshin rediyo, De Venus Bar, filin wasa na Uyo da sauran wuraren sayar da tikitin kallon wasan kwallon kafa
  • Hukumar NFF ta alkawarta raba rigunan Super Eagles ga magoya baya 500 na farko da suka samu tikitin kallon wasan da za a i

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Uyo, Akwa Ibom - Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta shirya karawa ƴan wasan Super Eagles karfi a wasan da za su yi a yau Talata 25 ga watan Maris, 2025.

Kara karanta wannan

2027: Ta fara tsami tsakanin ƴan adawa, burin Atiku da maganar yanki na son ta da kura

Gwamnatin jihar ta sanar da bayar da tikiti kyauta ga magoya bayan da za su halarci wasan tsakanin Super Eagles da Zimbabwe.

Gwamna zai ba ƴan kallo tikiti kyauta domin goyon bayan Super Eagles
Gwamna Umo Eno zai raba tikiti kyauta ga ƴan kallo domin wasan Super Eagles a Akwa Ibom. Hoto: Pastor Umo Eno.
Asali: Facebook

Super Eagles: Gwamna Uno zai raba tikiti kyauta

Wannan na kunshe a wata sanarwa da sakataren watsa labarai na gwamna Umo Eno, Ekerete Udoh ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun da farko, hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta yi alkawarin raba rigunan Super Eagles ga magoya baya 500 na farko da suka samu tikiti don halartar wasan.

Hakan zai karawa ƴan kwallon da magoya bayansu karfin guiwa wurin kara zagewa domin samun nasara a wasan.

A sanarwar da kwamishinan wasanni na jihar, Paul Bassey ya sanyawa hannu ya ce Gwamna Umo Eno ya sayi dukkan tikiti 30,000 don wasan da za a buga yau Talata 25 ga watan Maris, 2025.

Kwamishinan ya ce za a buga wasan ne a kasaitaccen filin wasa na Godswill Akpabio da ke birnin Uyo.

Kara karanta wannan

Bayan barazanar dokar ta baci a Kano, Aminu Ado Bayero ya gana da Wike

Gwamna ya bukaci ba Super Eagles goyon baya a wasansu na yau Talata
Gwamna Umo Eno ya bukaci hadin kai a wasan Super Eagles inda zai raba tikiti kyauta. Hoto: Pastor Umo Eno.
Asali: Twitter

Matsalar da Super Eagles ke ciki a yanzu

Bassey ya bayyana cewa tikitin kyauta za a raba a wurare daban-daban kamar tashoshin rediyo, 'De Venus Bar' da ke hanyar filin wasan da cikin filin wasa na Uyo da kuma wuraren sayar da tikiti.

Super Eagles za su kara da Zimbabwe a wasa na shida a gasar neman cancantar shiga cin kofin duniya.

Kungiyar na cikin matsala bayan gazawa a wasanni hudu na farko, ciki har da canjaras 1-1 da Zimbabwe a watan Nuwambar 2023.

Nasara daya tilo da Najeriya ta samu a gasar ita ce wadda suka yi da Rwanda ranar Juma’a 21 ga watan Maris, 2025.

Super Eagles na matsayi na hudu a rukunin neman cancantar shiga gasar da maki shida daga wasanni biyar.

Idan Najeriya ta yi nasara kan Zimbabwe, za ta samu karin damar samun cancanta, amma sabanin haka zai kara dagula yunkurinta na zuwa gasar cin kofin duniya ta 2026.

Kara karanta wannan

Nasarori 3 da Nyesom Wike ya samu a cikin kwanaki 3 a siyasar jam'iyyar PDP

An saki jadawalin gasar AFCON ta 2025

A baya, mun ba ku labarin cewa hukumar CAF ta fitar da jadawalin wasannin rukunai na gasar cin Kofin Nahiyar Afrika ta 2025.

Za a gudanar da gasar daga ranar 21 ga Disamba 2025 zuwa 18 ga Janairu 2026 mai zuwa a kasar Morocco da ke Arewacin Afirka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng