Marcelo: Shahararren Tsohon Dan Wasan Real Madrid Ya Yi Ritaya daga Buga Kwallon Kafa

Marcelo: Shahararren Tsohon Dan Wasan Real Madrid Ya Yi Ritaya daga Buga Kwallon Kafa

  • Shahararren ɗan wasan Real Madrid, Marcelo Jr., ya sanar da yin ritaya daga kwallon kafa bayan buga wasanni 546 da lashe kofuna 25
  • An rahoto cewa Marcelo ya lashe kofin zakarun Turai biyar tare da Real Madrid da gasar La Liga shida a tsawon kakar wasanni 16
  • Shugaban Real Madrid, Florentino Perez, ya bayyana Marcelo a matsayin daya daga cikin manyan ‘yan wasan baya a tarihin ƙungiyar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Madrid - Tsohon shahararren ɗan wasan Real Madrid, Marcelo, ya sanar da yin ritaya daga kwallon kafa yana da shekara 36 a duniya.

Marcelo ya buga wasanni 546 a tsawon kakar wasanni 16 da ya yi tare da Real Madrid, inda ya lashe kofin UEFA Champions League sau biyar.

Mercelo ya yi magana yayin da ya yi ritaya daga buga kwallon kafa
Mercelo, fitaccen dan wasan Real Madrid ya yi ritaya daga buga kwallon kafa. Hoto: @MarceloM12
Asali: Twitter

Mercelo ya sanar da yin ritaya daga kwallo

Kara karanta wannan

"Mutuwa mai yankar ƙauna": Matashiyar jarumar fina finai ta riga mu gidan gaskiya

Jaridar Euro Sport ta bayyana cewa Marcelo ya lashe gasar La Liga sau shida a Madrid tare da buga wa ƙasar Brazil wasa har sau 58.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Na zo Real Madrid ina da shekara 18. A yau zan iya alfahari da cewa ni ɗan Real Madrid ne na gaskiya,"

inji Marcelo.

A cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar 6 ga Fabrairu, 2025, Marcelo ya ce:

"Kaka 16, kofuna 25, Champions League biyar, ɗaya daga cikin kyaftin din 'yan wasa, da lokuta masu cike da tarihi a Bernabeu. Lallai an sha fama!"
"Da wannan ne na rufe babin rayuwata na matsayin ɗan wasa, amma har yanzu ina da abubuwan da zan yi a harkar kwallon kafa. Na gode kwarai."

Zaman Marcelo a Real Madrid da tafiyarsa

Marcelo ya koma Real Madrid a shekarar 2007 yana da shekara 18 daga kungiyar kwallon kafa ta Fluminense da ke Brazil.

Kara karanta wannan

Barazanar tsaro: An kama 'yan kasashen waje 165 da shirin kulla makirci a Najeriya

Ya kasance ɗan wasan da ke tashe a daya daga cikin lokuta mafi nasara a tarihin Real Madrid. Ya zama kyaftin din ƙungiyar a 2021.

Marcelo ya bar Real Madrid a 2022 inda ya koma Olympiacos, amma ya bar kungiyar bayan watanni biyar tare da komawa kungiyarsa ta farko, Fluminense.

'Real Madrid gidan Mercelo ce' - Perez

Shugaban Real Madrid, Florentino Perez, ya ce Marcelo yana daya daga cikin manyan ‘yan wasan baya a tarihin ƙungiyar da ma duniya baki ɗaya.

Perez ya ƙara da cewa:

"Tsawon lokaci muna jin dadin ganin Marcelo yana taka leda a kungiyarmu. Real Madrid za ta kasance gidansa har abada."

Marcelo ya samu matsala da kocin Madrid

A wani labarin, mun ruwaito yadda, dan wasan bayan Real Madrid, Marcelo Viera Jr., ya samu sabani da kocin kungiyar, Zinedine Zidane.

Rahotanni sun ce a ranar Laraba, 12 ga Mayu, 2021, Marcelo ya yi gardama da Zidane yayin da ake atisaye.

Kara karanta wannan

Ronaldo ya ce ya fi kowa iya kwallo a tarihin duniya, ya fadi dalilin rashin zuwansa Barce

Sakamakon wannan gardamar ne aka ce Zidane ya cire Marcelo daga jerin ‘yan wasan da za su buga wasan Real Madrid da Granada.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.