Zidane ya tsige Tauraro daga sahun ‘Yan wasan Real Madrid saboda ya yi masa gardama

Zidane ya tsige Tauraro daga sahun ‘Yan wasan Real Madrid saboda ya yi masa gardama

- Marcelo Jr. ya samu sabani da kocin kungiyar Real Madrid, Zinedine Zidane

- Hakan ya jawo cire ‘Dan kwallon daga cikin wadanda za su buga wasan yau

- Marcelo ya koka a kan salon kwallon Zidane da yadda ba a sa shi a wasanni

‘Dan wasan bayan kungiyar Real Madrid, Marcelo Viera Jr. ya samu kan shi a sabuwar matsala bayan sabanin da ya shiga tsakaninsa da Zinedine Zidane.

A ranar Laraba, 12 ga watan Mayu, 2021, jaridar goal.com ta fitar da rahoto cewa Marcelo Jr. ya yi wa babban mai horas da ‘yan wasan Real Madrid gardama.

Abin da ya biyo baya shi ne kocin kungiyar kwallon kafan na Sifen, Zinedine Zidane, ya cire shi daga sahun wadanda za su buga wasan daren yau da Granada.

KU KARANTA: An kai wa motar 'Yan wasan Real Madrid hari a Liverpool

Ganin cewa Ferland Mendy bai da lafiya, ba zai iya sake buga wani wasa a kakar bana ba, an yi ta tunanin cewa Marcelo zai karbi wurinsa a bayan Real Madrid.

A lokacin da Real Madrid ke shirin buga muhimmin wasa yau a filin Nuevo Estadio de Los Carmenes, sai aka ji cewa za a tafi birnin Granada babu Marcelo.

Abubuwa ba su tafiya daidai wajen ‘dan wasan na kasar Brazil a shekarar nan saboda salon buga kwallon Zidane da yadda Marcelo ya zama ‘dan kallo a Madrid.

Da aka zo atisaye a ranar Talata, ‘dan wasan bayan ya soki yadda Zinedine Zidane yake jan ragamar ‘yan wasan Real Madrid, wanda hakan ya kawo rikici.

KU KARANTA: Mun rabu da Jose Mourinho - Tottenham

Zidane ya tsige Tauraro daga sahun‘Yan wasan Real Madrid saboda ya yi masa gardama
'Dan wasan Real Madrid, Marcelo da Zinedine Zidane Hoto: www.goal.com
Asali: UGC

An yi tunanin buguwar da tauraron ya samu a wasan Sevilla ne zai hana shi buga wasan yau Alhamis, amma an gano sabani ne ya shiga tsakaninsa da kocin.

A halin yanzu ‘yan wasan bayan hudu rak suka ragewa Zidane, ragowar duk suna fama da jinya.

Ku na da labari kungiyar Manchester City ce ta sake samun nasarar cin gasar kofin EFL watau Carabao a filin wasan kwallon kafa na Wembley a shekarar bana.

Wannan gagarumar nasara ta na nufin Manchester City ta shafe shekaru hudu a jere ta na lashe gasar karamin kofin, abin da Liverpool ta taba yi a shekarun 1980s.

Asali: Legit.ng

Online view pixel