'Yan Wasan Najeriya 6 da Suka Taba Lashe Kyautar Gwarzon Kwallon Kafan Afirka

'Yan Wasan Najeriya 6 da Suka Taba Lashe Kyautar Gwarzon Kwallon Kafan Afirka

  • A ranar Litinin 16 ga watan Disambar 2024 aka gudanar da bikin ba da kyautar gwarzon dan wasan Nahiyar Afirka a birnin Marrakesh a kasar Morocco
  • Ademola Lookman daga Najeriya shi ya yi nasarar lashe kyautar ta wannan shekara a 2024 wanda ya zama ɗan wasa na 6 da ya lashe kyautar a Najeriya
  • Wannan rahoto zai kawo muku jerin yan wasan Najeriya da suka taba lashe kyautar tun daga 1993 har zuwa yau da muke shekarar 2024

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Marrakesh, Morocco - Dan wasan Najeriya, Ademola Lookman ya yi nasarar lashe kyautar gwarzon dan wasan Afirka ta shekarar 2024 da aka gudanar a kasar Morocco.

Lookman ya lashe kyautar bayan yin nasara kan sauran yan wasan Afirka da suka hada da Achraf Hakimi na kasar Morocco.

Kara karanta wannan

Kwana 1 ga barazanar Turji, an yi kazamar fada tsakanin yan bindiga, an rasa rayuka

Yan wasan Najeriya da suka lashe kyautar gwarzon dan wasan Afirka
Jerin yan wasan Najeriya da suka lashe kyautar gwarzon dan wasan Afirka a tarihi. Hoto: @Supereagles.
Asali: Twitter

Yan Najeriya da suka lashe kyautar gwarzon Afirka

Rahoton The Nation ya ruwaito cewa tsohon dan wasan Super Eagles kuma marigayi Rashidi Yakini shi ya fara lashe kyautar a shekarar 1993.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta yi bincike kan yan wasan Najeriya da suka lashe kyautar gwarzon dan wasan Nahiyar Afirka tun daga 1993 zuwa yau.

1. Rashidi Yakini (1993)

Rashidi Yakini shi ne dan wasan Najeriya na farko da ya fara lashe kyautar gwarzon dan wasan Afirka a 1993.

Yakini ya yi kaurin suna wurin cin kwallaye masu zafi a cikin fili inda ya zama mafi cin kwallo a gasar AFCON ta 1992.

Rashidi Yakini

2. Emmanuel Amunike (1994)

Emmanuel Amunike ya biyo bayan Yakini bayan lashe kyautar a shekarar 1994 duba da rawar da ya taka a lokacin.

Amunike ya yi tashe a gasar AFCON ta 1994, ya ci dukan kwallaye biyu da Najeriya ta doke Zambia a wasan karshe.

Kara karanta wannan

'Dan kwallon Najeriya da ya zamo zakaran Afrika ya fadi yadda aka yi masa dariya a baya

Emmanuel Amunike

3. Nwankwo Kanu (1996 da 1999)

Fitaccen dan wasan Najeriya, Nwankwo Kamu ya kafa tarihin zaman dan wasan farko da ya lashe kyautar har sau biyu a Najeriya.

Kanu ya yi bajinta sosai musamman a shekarun 1996 da 1999, ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Afrika gaba daya.

Kanu Nwankwo

4. Victor Ikpeba (1997)

Tsohon dan wasan Najeriya, Victor Ikpeba shi ma ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Afirka a shekarar 1997, cewar jaridar Punch.

Tsohon dan wasan Monaco a Faransa ya taka rawa a shekarar inda ya taimaka mata lashe gasar kofin kasar da na kalubale.

Victor Ikpeba

5. Victor Osimhen (2023)

Dan wasan kwallon kafar Najeriya, Victor Osimhen ya lashe kyautar zakarar dan kwallon kafa ta Nahiyar Afirka ta shekarar 2023.

Osimhen ya kara da gwarazan ‘yan wasa kamar su dan kasar Masar, Mohammed Salah da Achraf Hakimi na kasar Morocco.

Victor Osimhen ya kafa tarihi bayan Najeriya ta shafe shekaru 24 ba tare da lashe kyautar ba tun Kanu a 1999..

Kara karanta wannan

'Dan Najeriya ya lashe kyautar gwarzon ɗan kwallon Afirka na 2024

Osimhen ya zama gwarzon dan wasan Afirka

6. Ademola Lookman (2024)

Ademola Lookman ya yi nasarar lashe kyautar gwarzon ɗan wasan ƙwallon ƙafa na nahiyar Afirka na wannan shekara ta 2024.

Ɗan wasan tawagar Super Eagles da Atalanta yana ɗaya daga cikin ƴan kwallon da tauraruwarsu ke haskawa a Nahiyar Turai.

Kyautar gwarzon ɗan kwallon Afirka na 2024 za ta ci gaba da zama a Najeriya bayan Victor Osimhen ya lashe ta a bara watau 2023.

Ademola Lookman

Lookman ya tuna gwagwarmayar da ya sha

Kun ji cewa bayan lashe kyautar gwarzon dan wasan Afirka, Ademola Lookman a cikin jawabinsa ya yi dogon tunani kan gwagwarmayar rayuwarsa.

Ademola Lookman ya tuna wani babban kuskure da ya yi a shekarar 2020 lokacin yana buga wa Fulham wasa a gasar Firimiya ta Ingila.

Ademola ya ce ya yi yunkurin jefa bugun finareti wanda ya gaza saka kwallo a raga, lamarin da ya jawo suka daga kocinsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.