Dillalin Bogi Ya Damfari Barcelona, An Aika Masa Naira Biliyan 1.7 a Sayo Dan Wasa

Dillalin Bogi Ya Damfari Barcelona, An Aika Masa Naira Biliyan 1.7 a Sayo Dan Wasa

  • Lokacin da Barcelona ta ke kokarin sayo ‘dan wasan gaba daga Bayern Munchen, tsautsayi ya auka mata
  • Wani ya yi amfani da damar cinikin Robert Lewandowski wajen karbar £830,000 daga kungiyar kwallon
  • Sai da aka yi bincike aka gano ashe da dillalin karya aka yi ciniki, aka yi maza aka toshe asusunsa a banki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Spain - Wani abin mamaki ya faru a duniyar kwallon kafa, an samu wani dillalin karya da ya damfari kungiyar nan ta Barcelona.

Wani dillali na bogi ya damfari kungiyar kwallon kafan Barcelona da ke Sifen kudi har fam miliyan €1 watau £830,000 kenan a yau.

Barcelona
An nemi a damfari Barcelona wajen sayen Robert Lewandowski Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

'Dillalin' bogin Robert Lewandowski da Barcelona

Rahoton Daily Mail ya tabbatar da cewa wannan ‘dan damfara ya yi karyar shi ne dillalin da yake wakiltar Robert Lewandowski.

Kara karanta wannan

‘Yan APC da suka koma kuka da gwamnati saboda tsadar rayuwa a zamanin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kakar shekarar 2022 ne kungiyar ta sayo Robert Lewandowski daga Bayern Munchen kan €45m kuma tuni ya zura kwallaye 71.

An kusa damfarar kungiyar Barcelona

Sai dai abin da mutane ba su da labari shi ne an samu wani ya yaudari Barcelona, ya yi karyar ya na aiki Pini Zahavi, ya nemi kudi.

Zahavi shi ne asalin dillalin da yake wakiltar ‘dan wasan na kasar Poland a kasuwar cefane.

Wannan ja’iri ya bukaci a tura masa £830,000 ta wani asusun banki. Idan aka yi lissafi ya haura Naira biliyan 1.7 a kudin Najeriya.

Kungiyar Barcelona ta gano karyar dillali

Wani bincike da Cadena SER ta gudanar ya nuna mutumin bai da alaka ta kusa ko ta nesa da tsohon ‘dan wasan na Bayern Munich.

Da aka tuntubi Zahavi daga baya, ya tabbatarwa Barcelona cewa bai san mutumin da suka turawa kudi ba, ya sa aka rufe asusunsa.

Kara karanta wannan

'Ki ba ni Lokacinki': Bidiyon wakar Abdul D One da ya jawo ce ce ku ce a soshiyal midiya

Lamarin da Mirror UK ta ce ta kai dillalin bogin ya yi barazanar kai Barce kara a kungiyar UEFA idan ba a cika masa €250,000 ba.

A karshe kungiyar ta Barcelona ta iya dawo da kudinta, kuma ba ta bukaci a yi bincike ba lokacin Xavi yana horar da 'yan wasa.

An fusata tsohon tauraron Barcelona

Labari ya zo a baya cewa tsohon dan wasan Barcelona, Martin Braithwaite ya fusata da wulakancin da aka yi wa kungiyar Espanyol.

Braithwaite ya sha alwashin siyan kungiya Espanyol a Sifen domin sauya shugabanninta bayan matsalar da ya samu a Barcelona.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng