Messi, Ronaldo da Lewandoski ba za su ji dadin fasa bikin Ballon D’or ba

Messi, Ronaldo da Lewandoski ba za su ji dadin fasa bikin Ballon D’or ba

Annobar COVID-19 ta yi sanadiyyar jawo cikas a abubuwa da dama na rayuwa a shekarar 2020. Daga cikin bangarorin da annobar ta taba har da harkar wasanni.

A dalilin COVID-19 ne aka soke bikin Ballon d’Or da aka saba. An shafe shekaru 60 ana wannan biki, wannan shekara an samu canji a sakamakon halin da aka shiga.

Mun kawo jerin ‘yan wasan kwallon kafan da ake ganin cewa wannan mataki da aka dauka ba zai yi masu dadi ba. Watakila da sun yi nasarar lashe kyautar bana.

1. Lionel Messi

Lionel Messi ba ya bukatar gabatarwa a Duniyar kwallon kafa. ‘Dan wasan ne ya yi nasara a 2019 inda ya lashe kofinsa na shida.

A shekarar nan, Messi ya zura kwallaye 25 a gasar La-liga, bayan haka ya yi sanadiyyar da kungiyar Barcelona ta ci kwallaye 21.

KU KARANTA: Babu bikin Galar Ballon D ' or - L' equipe

Messi. Ronaldo da Lewandoski ba za su ji dadin fasa bikin Ballon D’or ba
Lewandowski bai taba cin kofin ba Hoto: FIFA
Asali: Getty Images

2. Cristiano Ronaldo

A shekarar nan Cristiano Ronaldo ya ci kwallayen da za su dade a tarihin Juventus. Sai dai har yanzu bai bar tambari a gasar Turai ba tukuna.

Ko da cewa Cristiano Ronaldo bai fara kakar bana yadda ya so ba, daga baya abubuwa sun mike masa, ya kuma jefa kwallaye 30 a Seria A.

3. Robert Lewandowski

Wani gwarzon ‘dan wasa shi ne Robert Lewandowski wanda ya zurawa Bayern Munich kwallaye fiye da 20 a gasar gidan shekarar nan.

Bayan ‘dan kwallon ya kai kungiyarsa ga nasarar lashe kofi biyu, shi ne wanda ya fi kowane ‘dan wasa zura kwallaye a gasar Nahiyar Turai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel