'Yan Sanda Sun Cafke Dan Wasan Manchester City, Ana Zargin Ya Saci Wayar Salula

'Yan Sanda Sun Cafke Dan Wasan Manchester City, Ana Zargin Ya Saci Wayar Salula

  • Rahotanni sun ce an kama wani dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City a kasar Spain bisa zargin sata a watan jiya
  • An ce an kama Matheus Nunes ne a gidan rawa na La Riviera da ke Madrid a ranar 8 ga watan Satumba bisa zargin satar wayar wani mutum
  • Ya kasance yana hutun karshen mako tare da abokansa a babban birnin Spain bayan an cire shi daga cikin tawagar Portugal a hutun kasa da kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Spain - A watan da ya gabata ne hukumomin Spain suka kama wani dan wasan Manchester City sakamakon wata rigima da ta kacame a wani gidan rawa.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Yobe, sufetan 'yan sanda ya kashe wani mutumi kan N200

A cewar rahotanni, 'yan sandan Spain sun kama Matheus Nunes a gidan rawa na La Riviera da ke Madrid bayan zargin satar wayar salula.

'Yan sanda sun kama dan wasan Manchester City kan zargin satar waya a gidan rawa
'Yan sandan Spain sun cafke dan wasan Manchester City kan zargin satar waya a gidan rawa. Hoto: Visionhaus, Carl Recine
Asali: Getty Images

Me ya faru aka kama Nunes?

Bisa ga rahoton jaridar El Mundo, Nunes ya na hutun karshen mako tare da abokansa a babban birnin Spain bayan ya gaza shiga cikin tawagar Portugal lokacin da abin ya faru.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama dan wasan ne da karfe 5:30 na safe kuma rahoton ‘yan sanda ya ce ya kwace wayar wani mutum mai shekaru 58 a bandakin gidan rawar.

A cewar dan wasan, mutumin ne ya yi yunkurin daukar hotonsa ba tare da izini ba wanda hakan ya sa ya kwace wayarsa.

An tsare dan wasan Man City

Nan take mutumin ya sanar da ‘yan sanda inda daga bisani suka sami wayar da ake magana kanta a cikin dakin tauraron na Manchester City.

Kara karanta wannan

"Kar a karaya:" Goodluck Jonathan ya tura sakon karfafa gwiwa ga yan kasa

Wasu shaidun gani da ido kuma sun ce mutumin ne ya taba dan wasan da wayarsa, lamarin da ya sa shi ya kwace wayar bisa tunanin za a dauki hotonsa ba da izini ba.

Matashin dan wasan mai shekaru 25 ya shafe wani lokaci a bayan kanta kafin ba da belinsa gabanin fara shari'a inji rahoton Reuters.

Me zai faru da Matheus Nunes?

Ana sa ran Nunes zai fuskanci shari'a kan lamarin amma zai ci gaba da zama tare da Manchester City kafin nan.

Dan wasan na Portugal ya shiga tawagar Man City a karawar da ta yi da Slovan Bratislava a daren Talata a gasar cin kofin zakarun Turai kuma an ganshi yana taka leda a ranar Asabar.

Man City ta lashe gasar Premier

A wani labarin kuma, mun ruwaito cewa Manchester City kafa sabon tarihi bayan da ta lashe kofin gasar Premier shekarar 2023/2024, kofin da ta daga karo na hudu a jere.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu bayan sace jariri dan kwanaki 7 a gidan suna

Phil Foden ya zura wa Man City kwallaye biyu yayin da shi ma Rodri ya zura kwallo daya, wanda ya ba tawagar Pep Guardiola damar lashe kofin karo na shida a cikin kaka bakwai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.