Manchester City ta fi kowace kungiya tara 'yan kwallo mafiya tsada a duniya
Kungiyar Manchester City wadda ta lashe gasar Premier League ta Ingila a bara, ta kasance a kan sahu na gaba cikin jerin kungiyoyin kwallon kafa da suka tara 'yan kwallo mafiya tsada a duniya a yanzu.
Manchester City ta kasance mai rike da kambun kungiyar kwallon kafa mai tarin manyan 'yan kwallon kafa wanda gamayyar kudinsu ta dara ta kowace kungiya tsada a doron kasa. Kungiyar dai ta kashe kimanin Fan Miliyan 906 wajen cefanen manyan wasa.
Babu shakka kungiyar ta yi wa sauran manyan kungiyoyin kwallon kafa sa'anninta fintikau irin su PSG, wadda ta sayi babban dan wasan nan daga kungiyar Barcelona, Neymar a kan makudan kudi da kuma kungiyar Real Madrid wadda ta baje arzikin ta wajen cefanen dan wasa Eden Hazard daga kungiyar kwallon kafa ta Chelsea.
Manchester City dai ta fidda makudan kudade wajen cefanen manyan 'yan wasa irin su, Kevin De Bruyne, Kyle Walker, Riyad Mahrez, John Stones, Aymeric Laporte, Joao Cancelo, Raheem Sterling da makamantansu.
KARANTA KUMA: Ramaphosa ya yi Allah wadai kan hare-haren da ake yiwa baki a Afirka ta Kudu
A rahoton da shafin UK Mirror mai lura da sha'anin kwallon kafa ya gabatar, ya fidda jerin kungiyoyin kwallo kafa 20 da suka hadar da manyan kungiyoyi na kasashen Turai daban-daban wadanda suka fi kowanne tara 'yan kwallo mafi tsada a duniya.
An samu kungiyoyin kwallon kafa guda biyar da ke buga gasar Firemiyar Ingila da suka shiga cikin sahun goman farko ta fuskar tara 'yan kwallon kafa mafi tsada.
Ga dai yadda jeranton ya kasance:
1. Manchester City - £909m
2. Paris Saint-Germain - £819m
3. Real Madrid - £809m
4. Manchester United - £673m
5. Juventus - £645m
6. Barcelona - £625m
7. Liverpool - £573m
8. Chelsea - £503m
9. Atletico Madrid - £494m
10. Arsenal - £447m
11. Everton - £436m
12. Tottenham - £417m
13. AC Milan - £366m
14. Inter Milan - £326m
15. Bayern Munich - £316m
16. Monaco - £312m
17. Napoli - £292m
18. Borussia Dortmund - £288m
19. Leicester City - £280m
20. Valencia - £239m
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng