Kocin Ingila ya kira ‘Dan kwallon Kungiyar Arsenal Saka a karon farko

Kocin Ingila ya kira ‘Dan kwallon Kungiyar Arsenal Saka a karon farko

- ‘Dan wasa Bukayo Saka ya tabbatar da cewa zai bugawa kasar Ingila

- Wannan ne karon farko da Matashin ‘dan kwallon zai wakilci kasarsa

- Iyayen Saka ‘Yan Najeriya ne, amma ya ki yarda ya bugawa Najeriya

‘Dan wasan gaban Arsenal, Bukayo Saka, ya samu gayyatar farko daga mai horas da ‘yan kwallon kasar Ingila a matsayin babban ‘dan wasan kwallon kafan kasar.

Bukayo Saka zai iya bugawa tawagar Three Lions a wasansu da za su yi da kasashen Wales, Belgium and Denmark a cikin ‘yan kwanaki kadan masu zuwa.

Wannan gayyata da Ingila ta yi wa Saka ta na nufin ya zabi kasar Turan a maimakon asalinsa Najeriya.

KU KARANTA: 'Dan Najeriya zai bugawa Real Madrid

Saka ya na cikin matasan da Koci Mikel Arteta ya ke ji da su a kungiyar Arsenal, kuma ya na cikin wadanda ake yi wa kallon manyan gobe a wasan kwallon kafa.

An haifi wannan matashi ne shekaru 19 da su ka wuce a birnin Landan. Asalin iyayen ‘dan wasan kwallon mutanen Najeriya ne wadanda su ka tare a kasar waje.

Kafin yanzu Bukayo Saka ya bugawa Ingila a matakin U16, U17, U18, U19 da kuma U21.

A baya kungiyar NFF ta Najeriya ta ce ba za ta yi kokarin lallabar ya bugawa kasarsa ta asali kwallo ba, Amaju Pinnick ya ce Super Eagles ta na da ‘yan wasa.

KU KARANTA: Abin da ya sa na zabi Barcelona - Dest

Kocin Ingila ya kira ‘Dan kwallon Kungiyar Arsenal Saka a karon farko
B. Saka Hoto: Premier League
Asali: UGC

“Mu na da ‘yan wasa rututu masu tasowa da su ke buga wurinsa, kuma su na kokari.” Inji Pinnick.

“Mu na da taurari a ko ina, saboda haka ba za mu je mu na rokon wani ya bugawa Najeriya ba.” Shugaban NFF ya ce idan sun cancanta, za su sa rigar Najeriya.

Kafin yanzu ‘yan wasan Chelsea Fikayo Tomori da Tammy Abraham sun kubucewa Super Eagles.

A makon nan ne labari ya zo mana cewa sabon ‘Dan wasan tsakiyan Liverpool watau Thiago Alcantara ya kamu da Coronavirus daga zuwansa kasar Ingila.

Kungiyar Liverpool ta bayyana cewa sabon ‘dan kwallon da ta sayo ya killace kansa yanzu

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel