Hadari: 'Dan Takarar 2023, Obi Ya Ziyarci Tauraron Super Eagles, Tijjani Babangida Yana Jinya

Hadari: 'Dan Takarar 2023, Obi Ya Ziyarci Tauraron Super Eagles, Tijjani Babangida Yana Jinya

  • Yayin da tsohon dan wasan Najeriya, Tijjani Babangida ya gamu da hatsari, dan takarar shugaban kasa, Peter Obi ya ziyarce shi
  • Obi ya kai ziyarar a yau Alhamis inda ya ce ya dauki matakin ne domin jajantawa Babangida kan rashin da ya tafka a hatsarin mota
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa musamman a shafinsa na X a yau Alhamis 7 ga watan Yuni 2024

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna – Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar LP, Peter Obi ya ziyarci Tijjani Babangida a jihar Kaduna.

Obi ya zaiyarci tsohon dan wasan Najeriya ne bayan ya gamu da hatsarin mota da iyalansa a kan hanyar Kaduna zuwa Zaria.

Kara karanta wannan

Kaduna: An shiga tashin hankali, wata amarya ta datse mazakutar angonta

Dan takarar shugaban kasa ya yi tattaki zuwa Kaduna domin ziyartar Tijjani Babangida
Peter Obi ya ziyarci Tijjani Babangida a jihar Kaduna kan iftila'in da ya faru da shi. Hoto: @PeterObi.
Asali: Twitter

Kaduna: Obi ya jajantawa Tijjani Babangida

'Dan takarar shugaban kasar ya kai ziyarar a yau Alhamis 6 ga watan Yuni kamar yadda ya bayyana a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ya kai masa ziyara domin jajanta masa kan rashin dansa da kaninsa bayan hatsarin da ya afku da shi da kuma matarsa.

Jawabin Obi bayan haduwa da Babangida

“A yau, na ziyarci tsohon dan wasan Najeriya, Tijjani Babangida wanda ya gamu da hatsarin mota a watan jiya a jihar Kaduna.”
“Na ziyarce shi ne domin jajanta masa kan rashin dansa da kuma kaninsa, Ibrahim Babangida wanda tsohon dan wasan Najeriya ne shi ma.”

- Peter Obi

Obi ya shawarci Tijjani Babangida kan jarabawar

Obi ya shawarci Tijjani Babangida da ka da ya bari jarabawar da ta same shi ta saka shi cire rai a rayuwa.

Kara karanta wannan

"Na koyi darasi": Obasanjo ya fadi yadda ya ƙi amincewa da taimakon tsohon Sarki a gidan kaso

Ya ce irin wadannan fitattun 'yan kwallon kafa sun cancanci goyon baya daga al'umma kan gudunmawar da suka bayar.

Tijjani Babangida ya rasa dansa a hatsari

A wani labarin, kun ji cewa tsohuwar jarumar fina-finan Kannywood, Maryam Waziri ta gamu da hatsarin mota a jihar Kaduna yayin da ta rasa ɗanta.

An sanar da cewa Maryam ta rasa wasu ɓangarori na jikinta musamman a fuska da suka haɗa da ido da kuma kunne.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.