Tijjani Babangida ya shawarci Iheancho daya tafi sojan haya wata ƙungiya
Shahararren tsohon dan wasan Super Eagles Tijjani Babangida yace kamata yayi dan wasan Najeriyan mai tashe Kelechi Iheanacho ya tattauna da kocin Manchester City Pep Guardiola dangane da yiwuwar cigaba da zamansa a kungiyar.
Babangida ya bayyana haka ne sakamakon zuwan sabon dan wasa Gabriel Jesus kungiyar ta Man City, wanda zai zama barazana ga Iheanacho, musamman ganin yadda dukkaninsu yan wasan gaba ne.
Kelechi Iheancho wanda ya buga wasanni 38, kuma ya ci kwallaye 12 bai buga wasanni biyun da kungiyar ta buga a kwanan nan ba tun bayan zuwan Jesus kungiyar. Babangida na ganin muddin aka cigaba da haka, dan wasan Najeriyan zai samu matsala musamman yayin da Najeriya ke kokarin shiga gasar cin kwallon Duniya na 2018 a kasar Rasha.
KU KARANTA:Sarakuna da gwamnonin Arewa sun tattauna lamarin tsaro a yankin
A ra’ayin Babangida, duba da shekarun dan wasan, kamata yayi Iheancho ya tafi sojan haya zuwa wata kungiya, inda zai samu damar warwarewa da kara gogewa ta hanyar buga wasanni da dayawa, hakan zai yi sanadiyyar dawowarsa kungiyar ta Man City da karfinsa.
“shawarar da zan baiwa Iheancho itace, ya zauna da Pep Guardiola su tattauna yiwuwar zamansa a kungiyar, saboda maganan gaskiya itace zuwan Gabriel Jesus kungiyar zai zamo barazana ga Iheanacho, wanda ka iya fitar da shi daga jerin yan wasan dake buga wasanni a kowane lokaci. Don haka nake ganin barinsa kungiyar zuwa sojan haya wata kungiya shine mafi alheri ga dan wasan, saboda yana bukatar samun buga wasanni da dama, da haka ne zai samu gogewa, kuma suma Man City sai su fi son shi a haka.” Inji Babangida yayin da yake tattaunawa da jaridar Daily Trust.
Sai dai ra’ayin Babangida yaci karo da na Mahaifin Kelechi Iheanacho, yayin da mahaifin dan wasan y adage akan lallai yaron nasa ba zai bar kungiyar Manchester City ba. Inda yace “Kelechi na jin dadi a kungiyar, kuma a shirye yake ya fafata da sauran yan wasan wajen neman gurbin buga wasanni. Don haka ba zai tafi wata kungiya ba da sunan sojan haya.”
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng