Super Eagles: Victor Osimhen Ba Zai Buga Wasannin Shiga Gasar Cin Kofin Duniya Ba

Super Eagles: Victor Osimhen Ba Zai Buga Wasannin Shiga Gasar Cin Kofin Duniya Ba

  • Fitaccen dan wasan gaba na Najeriya, Victor Osimhen ba zai buga wasanni biyu na neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya ba
  • Hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta bayyana cewa Osimhen ba zai buga wasan Super Eagles da Afrika ta Kudu da kuma Ivory Coast ba
  • NFF ta ce dan wasan na Napoli ya samu rauni wanda zai tilasta a ajiye shi, duk da ba ta bayar da cikakken bayani game da raunin ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Victor Osimhen ba zai buga wa Najeriya wasanni biyu na neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta 2026 ba saboda rauni, in ji hukumar kwallon kafa ta Najeriya.

Kara karanta wannan

Za a dakatar da Manchester United daga buga gasar Europa? INEOS ya yi magana

Hukumar NFF ta yi magana kan gasar cin kofin duniya
Osimhen ba zai buga wa Super Eagles wasannin shiga gasar cin kofin duniya ba. Hoto: @NGSuperEagles
Asali: Twitter

Wasanni biyu da Osimhen zai rasa

Hukumar ba ta bayar da cikakken bayani game da raunin ba amma ta ce dan wasan Napoli mai shekaru 25 zai yi jinyar makonni hudu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar ESPN ta ruwaito Osimhen ba zai buga karawar da Najeriya za ta yi da Afrika ta Kudu a Uyo ranar 7 ga watan Yuni.

Sannan tauraron zai rasa wasan Najeriya da Ivory Coast a Benin bayan kwanaki uku.

Rashin nasa ya kara wa kocin da aka nada a kwanan nan Finidi George nakasu a yunkurin da yake yi na ganin kungiyar ta Super Eagles ta dawo da martabarta yadda ya kamata.

Super Eagles ta tsara wasa da Osimhen

Najeriya na neman samun maki mafi yawa bayan da suka yi kunnen doki da Lesotho da Zimbabwe a wasannin share fage biyu da suka gabata, a cewae rahoton Arise News.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kinkimo namijin aikin da zai amfani mutane miliyan 30 a Najeriya

Sai dai kuma rashin Osimhen zai zama babban cikas ga damar da suka samu a karawarsu da tawagar 'yan wasan Afirka ta Kudu.

Tun da farko dai Finidi George ya saka Osimhen a cikin ‘yan wasa 23 da za su buga wasannin biyu amma rahoton kungiyar likitoci na baya-bayan nan ya tilasta sauya tsarin.

Man United ba za ta buga Europa ba?

A wani labarin, mun ruwaito cewa ana fargabar Manchester United ba za ta shiga gasar cin kofin Europa na kaka mai zuwa ba.

Wannan na zuwa bayan ganinmai mallakin United yana da iko kan wata kungiyar daban, abin da ya sabawa dokar kungiyar UEFA.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel