Za a Dakatar da Manchester United Daga Buga Gasar Europa? INEOS Ya Yi Magana

Za a Dakatar da Manchester United Daga Buga Gasar Europa? INEOS Ya Yi Magana

  • Rahotanni na nuni da cewa akwai yiyuwar Manchester United ba za ta buga gasar cin kofin Turai a kakar wasa mai zuwa ba
  • Kamfanin da ya mallaki United, INEOS, shi ne mamallakin kungiyar Nice wadda ita ma ta samu gurbin shiga gasar, abin da ya sabawa doka
  • To sai dai kuma, kamfanin na INEOS ya fitar da wata sanarwa yana mai nuna yakinin cewa zai cimma matsaya da UEFA kafin fara gasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Akwai shakku kan zuwan Manchester United a gasar cin kofin Europa a kakar wasa mai zuwa, duk da nasarar da ta yi a gasar cin kofin FA a karawarta da Manchester City.

Kara karanta wannan

Barcelona ta sallami kocinta Xavi Hernández, ta bayyana wanda zai maye gurbinsa

Nasarar da ta samu da ci 2-1 a filin wasa na Wembley, na nufin cewa tawagar Erik ten Hag za su buga gasar tare da Tottenham Hotspur.

Abin da ke shirin faruwa da Manchester United a gasar Europa
Akwai yiwuwar Manchester United ba za ta shiga gasar Europa a kaka mai zuwa ba. Hoto: @ManUtd
Asali: Twitter

To sai dai kuma, kamfanin INEOS da ya mallaki Man United shi ne ya mallaki kungiyar Nice da ke Faransa, abin da ya sabawa dokar busa Europa, in ji rahoton Goal.com.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da zai hana Man United buga Europa

Kungiyar Nice ta Faransa da Man United, wadanda ke karkashin ikon shugaban kamfanin INEOS, Sir Jim Ratcliffe, sun samu shiga gasar cin kofin Europa na kakar wasa mai zuwa.

Sai dai wata takardar dokoki na hukumar UEFA ta bayyana cewa kungiyoyin da suke karkashin ikon mutum daya ba za su iya shiga gasar Europa ba.

Abin da kamfanin INEOS ya ce

Kafar labaran Daily Mail ta ruwaito kamfanin INEOS ya fitar da sanarwa da ke cewa:

Kara karanta wannan

Notcoin: Dan Najeriya ya samu Naira miliyan 9 daga haƙar ma'adanan crypto a wayarsa

"Muna sane da matsayin kungiyoyin biyu kuma muna tattaunawa kai tsaye da UEFA.
"Muna da yakinin cewa za mu samu mafita gabanin fara gasar Europa a kakar wasa mai zuwa."

Abin da ke shirin faruwa da Man United

A cewar rahoton The Sun, an ji an cimma yarjejeniya da UEFA game da matsayin United da kuma Nice a gasar cin kofin Europa.

Wani shirin farko da INEOS ya so yi ya shafi kara yawan hannun jari zuwa sama da kaso 30, wanda hakan ke nufin cewa kungiyar United ce za ta keta dokokin UEFA.

A halin yanzu dai ko da kamfanin ya samu damar tsallake wannan matakin na yawan hannayen jari, ɗaya daga cikin kungiyoyin biyu ba zai buga gasar ta Europa.

Barcelona ta kori kocinta, Xavi

A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta yi hannun riga da mai horar da 'yan wasanta, Xavi Hernández.

Kara karanta wannan

"An gyara zalunci": 'Dan Sanusi II ya magantu da majalisa ta rusa masarautun Kano

Xavi wanda ya buga wa Barça wasanni sama da 700 a matsayin dan wasa, ya karbi ragamar horar da kungiyar a shekarar 2021.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel