Europa: Man Utd za ta hadu da Ajax a wasan karshe

Europa: Man Utd za ta hadu da Ajax a wasan karshe

- Man United ta kama hanyar daukar Kofin Europa na farko, wanda zai ba ta damar zuwa gasar Zakarun Turai ta Uefa, bayan da ta fitar da Celta Vigo ta je wasan karshe da za ta kara da Ajax, wadda ta yi waje da Lyon.

- An shiga wasan ne na biyu da nasarar kwallo daya da United ta jefa a ragar bakin nata a haduwarsu ta farko a Spaniya, inda Marouane Fellaini ya daga ragar bakin a wannan karawar da ka, bayan wata kwallo da Marcus Rashford ya dauko masa a minti na 17.

Legit.ng ta samu labarin cewa sai dai kuma Celta da take bukatar kwallo biyu, ta farke kwallon da aka zura mata a lokacin a minti na 85 ta hannun Facundo Roncaglia, abin da ya tayar da hankalin 'yan United, ya kuma zaburar da bakin.

Manchester United ta yi nasarar fitar da Celta Vigo da ci 2-1 jumulla wasa gida da waje. Kungiyoyin biyu sun kammala wasan da 'yan wasa goma-goma sakamakon korar da alkalin wasa ya yi wa Bailly da Roncaglia a minti na 87 sakamakon hatsaniyar da ta kaure tsakaninsu, wadda ta nemi rikita wasan.

Europa: Man Utd za ta hadu da Ajax a wasan karshe
Europa: Man Utd za ta hadu da Ajax a wasan karshe

KU KARANTA: Tsohon dan wasan duniya ya yabi JJ Okocha

Duk da cewa Lyon a gidanta ta doke Ajax a Faransa da ci 3-1, kungiyar ta Holland ce ta yi nasara saboda a karawarsu ta farko a Amsterdam, Ajax ta casa Lyon din 4-1, abin da ya sa sakamakon ya kasance 5-4 jumulla gida da waje.

Yanzu Manchester United za ta yi wasan karshe ranar 24 ga watan Mayu a Stockholm, da Ajax wadda ita kuma ta fitar da Lyon a daya wasan na kusa da karshe da ci 5-4 wasa gida da waje, inda wacce ta dauki kofin za ta samu gurbin gasar Zakarun Turai a kaka ta gaba.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel