Wasanni: Lionel Soccoia ya zama Mai horas da ‘Yan wasan Kano Pillars

Wasanni: Lionel Soccoia ya zama Mai horas da ‘Yan wasan Kano Pillars

- Lionel Emmanuel Soccoia zai horas da Kungiyar kwallon kafan Kano Pillars

- Gwamnatin Kano ta amince da nada Bafaranshen a matsayin Kocin kungiyar

- Emmanuel Soccoia zai tafi da Ibrahim Musa wanda dokar CAF ta yi wa cikas

Kungiyar wasan kwallon kafa na Kano Pillars da ke Najeriya, ta amince da nadin Lionel Emmanuel Soccoia a matsayin sabon kocinta.

Lionel Emmanuel Soccoia zai rika horas da ‘yan wasan kungiyar ta Kano, yayin da ake shirin buga wasannin zagaye na gasar nahiya.

A makon nan kungiyar Pillars ta fitar da sanarwar Lionel Soccoia ya yi na’am da kwantiragin shekara guda zuwa kakar shekarar badi.

KU KARANTA: 'Yan wasan Najeriya 4 sun kamu da cutar COVID-19

“Kocin ya na Najeriya, za a gabatar da shi gaban ‘yan jarida da sauran jama’a a ranar Laraba.” Inji mai magana da yawun kungiyar kwallon.

Rilwan Idris Malikawa ya yi wannan jawabi ne a ranar Talata, 21 ga watan Oktoba, 2020 kamar yadda Score Nigeria ta fitar da rahoto.

Kungiyar ta ce sabon kocin zai yi aiki da sauran masu horas da kungiyar a karkashin Ibrahim Musa wanda ya ke jan ragamar Kano Pillars.

Soccoia ya yi aiki a kasashe da dama wadanda su ka hada da Kamaru, Tanzaniya, Zambiya da kuma kasar Afrika ta Kudu har zuwa 2019.

KU KARANTA: 'Dan wasan PSG ya nemi ya tashi ya bar kungiya

Wasanni: Lionel Soccoia ya zama Mai horas da ‘Yan wasan Kano Pillars
Ganduje da Kano Pillars Hoto: soccernet.ng
Asali: UGC

Mai girma gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya amince da wannan nadin mukami na sabon koci da kungiyar ta yi.

Dokar CAF ta haramta wa Ibrahim Musa horas da ‘yan wasan saboda karancin satifiket, don haka kungiyar ta dauko hayar Bafaranshen.

A watan jiya ne ku ka ji cewa Najeriya ta kai mataki na 29 a jadawalin kasashen duniya wajen buga kwallon kafa da hukumar FIFA ta fitar.

Super Eagles ce ta uku a kaf Africa bayan Sanagal da kasar Tunisia da ke Arewacin nahiyar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel