Kalli irin barnar da aka tafka bayan wasa tsakanin Katsina United da Kano Pillars

Kalli irin barnar da aka tafka bayan wasa tsakanin Katsina United da Kano Pillars

A ranar Laraba, 15 ga watan Janairu ne aka fafata a wasan kwallon kafa tsakanin kungiyar Kano Pillars da Katsina United a filin wasa na Muhammadu Dikko dake garin Katsina, sai dai an tashi wasa baram baram.

Kungiyar Katsina United ta bayyana cewa rikicin ya fara ne a daidai lokacin da Tasiu Lawal ya zura kwallon a ragar Pillars a minti na 44, bayan Adelani na Pillars ya fara zuwa kwallo a ragar United a minti na 26.

KU KARANTA: Karamin yaro dan Fulani makiyayi ya gamu da ajalinsa a hannun miyagu a Kaduna

Kalli irin barnar da aka tafka bayan wasa tsakanin Katsina United da Kano Pillars
Kalli irin barnar da aka tafka bayan wasa tsakanin Katsina United da Kano Pillars
Asali: Facebook

Biyo bayan farkewar da United ta yi ne sai magoya bayan Kano Pillars suka fara tuge kujerun filin wasan suna jifan alkalan wasa da su, sa’annan suka fara fashe fashen gilasan tagogi, tare da banka ma wani sashin filin wasan wuta, inji hukumar Katsina United.

Sai dai Kano Pillars a nata bangaren ta koka kan rashin mutuncin da Katsina United ta yi mata, inda tace magoya bayan Katsina United sun kai ma yan wasanta hari, sun yi sace su tare da yin garkuwa da wasu daga cikinsu.

Kalli irin barnar da aka tafka bayan wasa tsakanin Katsina United da Kano Pillars
Kalli irin barnar da aka tafka bayan wasa tsakanin Katsina United da Kano Pillars
Asali: Facebook

Amma a nata martanin, Katsina United ta musanta zargin da Kano Pillars ta yi, kamar yadda mai maganda yawunta Wale Oye ya bayyana, inda yace babu wani dan wasa da aka yi garkuwa da shi a Katsina.

“Gaskiyar maganan shi ne Yansanda sun sharwarce yan wasan dukkanin kungiyoyin biyu tare da jami’ansu dasu jira a cikin filin wasan har sai sun fatattaki jama’a sun gyara hanya, daga bisani suka dawo suka raka kungiyoyin zuwa wajen filin wasan, sa’anann suka raga Kano Pillar har zuwa wani gari dake kusa da Daura.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel