NFF Ta Nada 'Dan Arewa a Matsayin Sabon Mai Horar da Tawagar Golden Eaglets Ta Nijeriya
- A ranar Juma’a ne tawagar Golden Eaglets ta samu sabon koci, Manu Garba wanda ya jagoranci tawagarsa ta lashe kofin duniya na 2013
- Wani bangare na aikin da ke jiran Garba shi ne shirya tawagar wajen buga gasar WAFU B ta 'yan kasa da shekara 17, da za a gudanar a Ghana
- Garba wanda ya fito daga Arewa ya horar da manyan ‘yan wasan Najeriya kamar Kelechi Iheanacho, Taiwo Awoniyi, Isaac Success
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta nada tsohon zakaran gasar cin kofin duniya na ‘yan kasa da shekaru 17, Manu Garba, a matsayin kocin kungiyar Golden Eaglets.
'Yan wasan da Garba ya horar
Wani dan jarida mai daukar hoto na FIFA da CAF, Adepoju Tobi Samuel ne ya bayyana nadin Garba a shafinsa na X a ranar Juma'a, 12 ga Afrilu.
A lokacin gasar cin kofin duniya na 'yan kasa da shekaru 17 na shekarar 2013 a hadaddiyar daular Larabawa, Garba ya jagoranci 'yan wasan Golden Eaglets da suka lashe kofin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga cikin 'yan wasan da suka saka burin Garba a lokacin ya zama gaskiya akwai Kelechi Iheanacho, Taiwo Awoniyi, Isaac Success, Musa Mohammed, Chidiebere Nwakali da Dele Alampasu.
Golden Eaglets ta daga kofin 2013
Tawagar ce ta kare a matsayi na biyu a gasar cin kofin Afrika na 'yan kasa da shekaru 17 da aka yi a Morocco bayan da Cote d'Ivoire ta doke su a bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Sai dai kungiyar ta lallasa Mexico da ci 6-1 a wasansu na farko, inda suka yi kunnen doki (3-3) da Sweden, sannan ta lallasa Iraki da ci 5-0.
A zagaye na 16, ta lallasa Iran da 4-1, ta ture Uruguay da 2-0 a wasan daf da na kusa da na karshe sannan ta lallasa Sweden da ci 3-0 a wasan kusa da na karshe, kafin daga bisani ta lallasa Mexico da maki daya a wasan karshe don daga gasar.
Ana sa ran Garba zai jagoranci shirye-shiryen kungiyar na gasar WAFU B ta 'yan kasa da shekaru 17, da zai gudana a Ghana.
Ronaldo ya taya Musulmi murnar Sallah
A wani labarin, Legit Hausa ta rahoto Cristiano Ronaldo ya taya Musulmi murnar karamar Sallah, tare da yi masu fatan alkairi.
Ronaldo ya wallafa sakon barka da Sallah ne a shafinsa na X watau Twitter a ranar Laraba, yana sanye da fararen tufafin larabawa.
Asali: Legit.ng