Kotu Ta Daure Tsohon Dan Wasan Barcelona, Dani Alves Shekaru 4 a Gidan Kaso Kan Wani Dalili
- Wata kotu da ke kasar Andalus ta yanke wa tsohon dan wasan Barcelona hukuncin daurin shekaru a gidan gyaran hali
- Ana zargin tsohon dan wasan Brazil, Dani Alves ta haikewa wata mata a gidan gada a birnin Barcelona da ke kasar
- Bayan sauraran dukkan korafe-korafen, alkalin kotun ya yanke wa Alves daurin shekaru hudu da watannin shida a gidan kaso
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Barcelona, Spain - Kotu ta yanke wa tsohon dan wasan kwallon kafa ta Barcelona, Dani Alves daurin shekaru hudu a gidan yari.
Kotun da ke kasar Andalus a yau Alhamis 22 ga watan Faburairu ta sami Alves da laifin haikewa wata mata a gidan gada, cewar Punch.
Wane hukunci kotun ta yanke kan Alves?
Bayan sauraran dukkan korafe-korafen daga ko wane bangare, alkalin kotun ya yanke wa Alves daurin shekaru hudu da watannin shida a gidan kaso.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har ila yau, bayan zaman kurkukun, dole ne Alves ya biya diyyar Yuro dubu 150 akan laifin cin zarafi ga matar., Cewar ESPN.
Tsohon dan wasan Barcelona ya yi fice a lokacin da ta ke buga tambola a kungiyar a matsayin mai tsaron baya.
Alves ya yi magana kan zargin
Lamarin ya faru ne a ranar 31 ga watan Disambar 2022 wanda ta zubar wa fitaccen dan wasan mutunci a idon duniya.
Alves bayan karanto tuhume-tuhumen da ake zarginsa ya musanta aikata laifin gaba daya, Goal.com ta tattaro.
Har ila yau, kotun ta yi hukuncin ne bisa shaidun da ta samu da kuma tabbaci daga wacce lamarin ya faru da ita.
Tun farko Alves ya musanta aikata hakan inda ya ce kawai sun hadu ne a cikin makewayi amma babu abin da ya faru tsakaninsu.
Tsohon dan wasan Bayern Munich ya mutu
Kun ji cewa tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich, Andreas Brehme ya riga mu gidan gaskiya.
Brehme kafin rasuwarsa da taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich da kuma Inter Milan ta kasar Italiya.
Marigayin shi ne ya zura kwallon da ta bai wa Jamus nasara a gasar cin kofin duniya a shekarar 1990.
Asali: Legit.ng