Mai Tsaron Gidan Ivory Coast Ya Yi Amfani da Laya a Wasan Karshe Na AFCON 2023? Gaskiya Ta Bayyana
- Ana zargin mai tsaron gidan Ivory Coast, Yahia Fofana, ya yi amfani da laya a wasan ƙarshe na gasar cin kofin Afrika (AFCON) tsakanin Super Eagles ta Najeriya
- A cikin wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta, mai tsaron gidan ya sa wani baƙin abu ɗaure a ƙugunsa da farar igiya
- Sai dai binciken gaskiya a faifan bidiyon ya nuna cewa mai tsaron gidan da ke cikin faifan bidiyon ba ɗan Ivory Coast bane Fofana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
An gano cewa bidiyon da mai tsaron gidan The Elephants na Ivory Coast, Yahia Fofana, ya yi amfani da laya a wasan ƙarshe da Super Eagles ta Najeriya, ya tabbata ƙarya ne.
Najeriya ta sha kashi a hannun Ivory Coast a wasan ƙarshe na gasar AFCON 2023 da ci 2-1 a ranar Lahadi, 11 ga watan Fabrairun 2023.
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, faifan bidiyon ya nuna wani mai tsaron gida sanye da riga mai lamba I6 da sunan “ASC JARRAF”.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai tsaron gidan yana da wani baƙin abu a manne a ƙugunsa da farar igiya.
Batun da ke faruwa ya jawo hankalin ƴan Najeriya da dama inda wasu ke kira ga hukumar ƙwalon ƙafa ta duniya (FIFA) da ta binciki zargin yin amfani da layar.
Me bincike ya ce kan bidiyon?
Binciken gaskiya ya nuna cewa mai tsaron gidan da ke a cikin bidiyon ba shine ɗan Ivory Coast ba, Yahia Fofana da ya buga wasa da Super Eagles.
Har ila yau, rubutun da ke kan rigar - ACF JARAAF (Association Sportive et Culturelle Jaraaf) na wata ƙungiyar ƙwallon ƙafa ce ta ƙasar Senegal da ke Dakar.
AFCON 2023: Ahmed Musa ya aike da sako mai ratsa zuciya bayan rashin nasarar Najeriya a wasan karshe
Fofana yana taka leda a matsayin mai tsaron gida a kulob ɗin Angers na Ligue 2 da ke ƙasar Faransa.
Kammalawa
An tabbatar da cewa faifan bidiyon ƙarya ne kuma ba mai tsaron gidan Ivory Coast bane kamar yadda aka yi ta yayatawa a shafukan sada zumunta.
Mai tsaron ragar da ke cikin faifan bidiyon yana taka leda ne a ƙungiyar da ke babban rukuni na ƙungiyoyin ƙwallon kafa na Senegal.
An haifi Fofana a ranar 21 ga Agusta, 2000, a Faransa ba Senegal ba.
Dalilin Rashin Nasarar Najeriya a Hannun Ivory Coast
A wani labarin kuma, kun ji cewa Jose Peseiro mai horar da tawagar ƴan wasan Super Eagles, ya aminta cewa ƴan wasan Ivory Coast sun nuna bajinta a wasan ƙarshe na cin kofin AFCON 2023.
Kocin ya bayyana cewa tawagar ƴan wasan sun fi ƙarfin Najeriya a wasan ƙarshen da aka yi na gasar kofin nahiyar Afirka (AFCON) a birnin Abidjan.
Asali: Legit.ng