AFCON: Mourinho Ya Fadi Kasar da Ya Ke So Ta Lashe Gasar, Ya Tura Sako Ga Abokinsa, Peseiro
- Jose Mourinho, tsohon kocin Manchester United ya bayyana kasar da ya ke so ta ci gasar AFCON da za a yi a yau Lahadi
- Mourinho ya ce ya na muradin tawagar Super Eagles ta lashe wasan karshen da za a gudanar a daren yau da Ivory Coast
- Wannan na zuwa ne yayin da Najeriya za ta kara da Ivory Coast a daren yau Lahadi 11 ga watan Faburairu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Tsohon kocin Chelsea da Mancheser United, Jose Mourinho ya bayyana kasar da ya ke so ta lashe gasar AFCON.
Mourinho ya ce ya na muradin tawagar Super Eagles ta lashe wasan karshen da za a gudanar a daren yau da mai masaukin baki, Ivory Coast.
Mene Mourinho ke cewa kan wasan Najeriya?
Kocin ya bayyana haka ne a yau Lahadi 11 ga watan Faburairu yayin hira da FIVE UK inda ya ce kocin Najeriya babban abokinsa ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da ya ke magana kan wasan a yau, Mourinho ya na so Super Eagles kocinta, Jose Peseiro su yi nasara.
A cewarsa:
“Mun taso da Peseiro inda muka hadu a Jami’a kullum muna tare na tsawon shekaru biyar.
“Babban abokina a wasan kwallon kafa yau zai buga wasan karshe, kocin Najeriya babban abokina ne mun taso tare.
“Mun yi karatu tare, mun je Jami’a tare, mun shafe shekaru biyar tare kuma mun bar Jami’a a lokaci daya, shi ne babban abokina a kwallon kafa, kuma yanzu ya samu daman kafa tarihi, kocin Portugal bai taba cin kofin AFCON ba.”
Hirar da aka yi da Mourinho
Wannan na zuwa ne yayin da Najeriya za ta kara da Ivory Coast a daren yau Lahadi 11 ga watan Faburairu da misalin karfe tara na dare.
Musa ya yi magana kan makomarsa
Kun ji cewa Kyaftin din tawagar Super Eagles, Ahmed Musa ya ce ba ya tsammanin barin kungiyar nan kusa.
Musa wanda ke neman cin kofin AFCON a karo na biyu bai taba buga ko da wasa daya ba a wannan gasa da ake yi a Ivory Coast.
Asali: Legit.ng