Najeriya vs Cote d'Ivoire: Shugaba Tinubu Ba Zai Halarci Wasan Karshe Na AFCON Ba, Bayanai Sun Fito
- Shugaba Bola Tinubu ya umurci mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima da ya jagoranci tawagar shugaban ƙasa zuwa wasan ƙarshe na AFCON
- Tinubu ya ba da umarnin goyon bayan Super Eagles yayin da za su fafata da ƙungiyar The Elephants ta Cote d'Ivoire a ranar Lahadi, 11 watan ga Fabrairu
- Shugaban ya buƙaci ƴan Najeriya da su nuna cikakken goyan baya wanda zai kai ga nasarar Super Eagles
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Fadar shugaban ƙasa, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ba zai halarci wasan ƙarshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka ba tsakanin Super Eagles da ƙungiyar The Elephants ta Cote d’Ivoire.
Tinubu ya umurci mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima da ya jagoranci tawagar shugaban ƙasa zuwa wasan ƙarshe na AFCON, a filin wasa na Alassane Ouattara da ke Abidjan a ranar Lahadi, 11 ga watan Fabrairu.
Stanley Nkwocha, babban mataimaki na musamman ga mataimakin shugaban ƙasa kan harkokin yada labarai da sadarwa ya bayyana hakan a wata sanarwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai ba da shawara na musamman kan Labarai da dabaru ga Shugaba Tinubu, Bayo Onanuga, shi ma ya tabbatar da hakan ta shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter).
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"Shugaba Tinubu ya yi imanin cewa kasancewar mataimakin shugaban ƙasa Shettima a wasan ƙarshen tare da tawagar, alama ce ta nuna goyon bayan gwamnati ga ƙungiyar da kuma jajircewa domin nasararsu."
Gwamnatin tarayya ta yi kira ga ƴan Najeriya da su haɗa kai domin marawa Super Eagles baya.
Shugaban ya kuma buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara zage damtse wajen ƙarfafa gwiwa tare da haifar da kishin ƙasa wanda zai sa ƙungiyar ta samu nasara.
Shugaba Tinubu zai lula zuwa kallon wasan ƙarshe na gasar cin kofin Afirka AFCON? Gaskiya ta bayyana
Karanta wasu abubuwa kan AFCON 2023
- Ahmed Musa da wani ɗan wasa zasu kafa muhimmin tarihi 1 idan Najeriya ta lashe kofin AFCON
- AFCON 2023: Gwamnatin Tinubu ta yi wa tawagar Super Eagles muhimmin alƙawari saboda kai wa wasan ƙarshe
- AFCON 2023: Tawagar Najeriya ta tsalalaka zuwa wasan ƙarshe bayan lallasa Afirika ta Kudu
Hanyar Doke Najeriya a Wasan Karshe Na AFCON
A wani labarin kuma, kun ji cewa kocin ƙungiyar The Elephants ta ƙasar Cote d'Ivoire ya yi magana kan hanyar doke Najeriya a wasan ƙarshe na AFCON 2023.
Emerse Fae ya bayyana cewa za su yi nazarin salon wasan Super Eagles domin yin nasara a kansu a wasan na ranar Lahadi, 11 ga watan Fabrairun 2024.
Asali: Legit.ng