AFCON 2023: Kocin Cote d'Ivoire Ya Fadi Hanyar da Za Su Bi Don Doke Najeriya a Wasan Karshe
- Emerse Fae, babban kocin ƙungiyar The Elephants ta Cote d’Ivoire, ya ƙuduri aniyar doke Super Eagles ta Najeriya a wasan ƙarshe na gasar cin kofin AFCON 2023
- Wasan da ake sa ran zai gudana ne a filin wasa na Alassane Quattara da ke Abidjan a ranar Lahadi 11 ga watan Fabrairu
- Fae ya ce zai yi nazari a kan wasan da Najeriya ta yi da dabarun da za ta bi, da nufin kawar da rashin nasarar da suka yi a hannun Super Eagles
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Abidjan, Cote d’Ivoire - Emerse Fae, babban kocin ƙungiyar The Elephants ta Cote d’Ivoire, ya ce zai samar da tsarin cin nasara ga ƙungiyarsa kan Super Eagles ta Najeriya a gasar cin kofin AFCON 2023.
Shugaba Tinubu zai lula zuwa kallon wasan ƙarshe na gasar cin kofin Afirka AFCON? Gaskiya ta bayyana
Cote d’Ivoire za ta kara da Najeriya a wasan ƙarshe na AFCON 2023 a filin wasa na Alassanne Quattara, Ebimpe, Abidjan a ranar Lahadi 11 ga Fabrairu (9:00 na dare agogon Najeriya).
Ƙasar wacce ta karɓi baƙuncin gasar ta doke Leopards ta DR Congo a wasan kusa da na ƙarshe da ci 1-0, inda za su fafata da Super Eagles.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za mu yi nazarin Najeriya - Fae
Da yake magana bayan nasarar da ƙungiyarsa ta samu a wasan kusa da na ƙarshe, Fae ya ce zai yi nazari kan ƙungiyar Super Eagles tare da tsara dabarun doke ƙungiyar wacce ta lashe gasar AFCON sau uku, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
A Kalamansa:
"Za mu yi nazari kan Najeriya, duk da cewa mun buga da su a matakin rukuni, za mu ga dabarun da za mu yi amfani da su a wasan ƙarshe."
Ku tuna cewa Super Eagles ta doke Cote d’Ivoire da ci 1-0 a lokacin da ƙungiyoyin biyu suka haɗu a rukunin farko a gasar.
Ahmed Musa Zai Kafa Tarihi a AFCON
A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan wasan gaba na Najeriya, Ahmed Musa yan ashirin kafa tarihi idan Najeriya ta samu nasarar lashe gasar AFCON 2023.
Ahmed Musa da Kenneth Omeruo za su zama ƴan wasan Najeriya da suka taɓa ƙasje kofin AFCON idan har Super Eagles ta yi nasara kan The Elephants ta Cote d'Ivoire a wasan ƙarshe na AFCON 2023.
Asali: Legit.ng