“Kada Ka Kalla Idan Kana da Hawan Jini”: Matashi Ya Bada Shawara Gabannin Wasan Najeriya Na Karshe
- Wani mutum ya ce zai fi kyautuwa mutum ya hakura da kallon wasan Najeriya da Cote d'Ivoire idan har kwakwalwarsa ba za ta iya daukar abun ba
- A cewar mutumin, zai fi kyau mutum ya bibiyi sakamakon wasan ta yanar gizo idan har ba zai iya shanye wasu tashin hankali ba idan aka ci Najeriya
- A kalla 'yan Najeriya biyar ne suka mutu bayan sun yanke jiki sun fadi a wasan kusa da karye na Najeriya da Afrika ta Kudu
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Wani mutumi ya bayar da muhimmiyar shawara ga wadanda suka san suna da hawan jini yayin da Najeriya ke shirin karawa da Ivory Coast.
Za a buga wasan karshe na gasar cin kofin Afrika a ranar Lahadi, 11 ga watan Fabrairu, amma mutumin ya ce zai fi kyautuwa idan wasu mutane suka bibiyi sakamakon wasan a yanar gizo.
A wani bidiyo da ya yada a TikTok, mutumin mai suna @justicecrack, ya dage cewa irin wannan wasan na 'dai'daita tunanin mutum kuma ba zai yi kyau ga mai hawan jini ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kalamansa:
"Yayin da muke murnar nasararmu yayin wasan Najeriya da Afrika ta Kudu a gasar AFCON na 2023 mun rasa wasu 'yan Najeriya wadanda suka mutu saboda bugawar zuciya yayin kallon wasan."
Hakika kafafen yada labarai sun cika da rahotannin wasu 'yan Najeriya da suka yanke jiki suka mutu a tsakiyar wasan, musamman ma lokacin da VAR da ta soke kwallon da Victor Osimhen ya ci.
Kalli bidiyon shawarar mutumin a kasa:
Jama'a sun yi martani
Lonwabo ya yi martani:
"Ba mu dauki abin da zai haka ba mu a Afrika ta Kudu."
@ESEYIN ya ce:
"Dole wani abu ya kashe dan adam. Ina da hawan jini kuma zan kalli wasan karshe. Nagode."
@Rita christy ta ce:
"Amma tsaya faaa. Wato da gaske Afrika ta Kudu ke son cin Najeriya? Allah ya kyauta yaran zamani."
AFCON: Shehu Sani ya shawarci mata kan mazajensu
A wani labarin, mun ji cewa tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya bai wa mata shawara don kare mazajensu daga mutuwa yayin kallon kwallo.
Sani ya shawarci matan da su kula sosai da mazajensu musamman wadanda suka san masoya harkon kwallon kafa ne.
Asali: Legit.ng