AFCON: Jerin Tawagar Kasashe 10 da Suka Tsallake Zuwa Zagaye Na 16
- A yayin da aka kammala zagayen farko na gasar kofin Nahiyar Afirka, kasashe 10 sun samu damar tsallakawa zuwa zagaye na 16
- Yayin da kuma ake jiran kammala wasan zagaye na rukunin E da F, ana sa ran kasashe hudu da suka zo a na uku za su iya zuwa mataki na gaba
- Najeriya, Masar, Senegal, Equatorial Guinea na daga cikin wadanda suka tsallake, yayin da aka kori Ghana, Algeria da sauran su daga gasar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
A daren ranar Larabar nan ne za a kawo karshen buga wasa a rukunoni na gasar cin kofin Nahiyar Afirka (AFCON2023), inda rukunin E da F za su fafata don zuwa zagaye na 16.
Yanzu dai tawagar kasashen 10 ne suka samu nasarar tsallakawa zuwa zagaye na 16, biyo bayan kammala wasannin rukunin A, B, C da D, amma ana kan jiran rukunin E da F.
Tawagar kasashen da ke rukunin E da F ne kawai ba su buga wasan karshe ba, inda Tunisia da Afrika ta Kudu ke kokarin tsallakawa zuwa mataki na gaba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yiyuwar kasar Ivory Coast ta tsallaka mataki na gaba
Ba iya kasashe biyu da ke saman teburin kowanne rukuni ne kaɗai suka tsallake zuwa zagaye na 16 ba, Business Day ta ruwaito.
Kasashe biyu mafi maki a cikin rukunonin shida ne suka tsallake zuwa zagaye na 16 tare da kuma ƙasashe hudu da suka zo a mataki na uku amma suka fi kowa kokari.
Da yiyuwar kasar Ivory Coast da ta karbi bakuncin gasar ta tsallake zuwa mataki na gaba, amma babu tabbas kan hakan, har sai an gama wasannin rukunonin E da F.
Kamaru za ta fafata da Najeriya ranar Asabar
A hannu daya kuma, tawagar Black Star ta kasar Ghana wacce ta lashe kofin har sau uku an kora ta gida daga gasar a wannan karon.
Ita ma Algeria, wacce ta dauki kofin har sau biyu ta tattara kayanta ta koma gida bayan shan kasa a hannun Mauritania a ranar Talata, inda wasan ya tashi 1-0.
Kamaru ta samu nasarar doke kasar Gambia da 3-2 kuma za ta fafata da Najeriya a ranar Asabar mai zuwa.
Yadda wasu kasashe suka sha da kyar
Vanguard ta ruwaito cewa Angola ta lallasa Burkina Faso da ci 2-0, amma dukansu sun tsallake zuwa zagaye na 16 saboda zama a saman teburin rukunin D.
Mauritania da ta doke Algeriya da ci daya mai ban haushi ta koma ta uku. Za su je zagaye na 16 ne cikin kasashen da suka zo na uku amma suka fi saura kokari.
A ranar Asabar 27 ga watan Janairu ne za a fara buga zagaye na 16 na gasar.
Ga jerin tawagar kasashen da suka tsallake:
- Cape Verde
- Senegal
- Equatorial Guinea
- Najeriya
- Masar
- Kamaru
- Guinea
- Angola
- Burkina Faso
- Mauritania, da
- Mali
Jerin kasashen da aka kora daga gasar:
- Guinea-Bissau
- Mozambique
- Gambia
- Algeria
- Ghana
AFCON: Kwankwaso ya taya tawagar Najeriya murna
A wani labarin makamancin wannan, jagoran jam'iyyar NNPP na kasa, Dr. Rabiu Kwankwaso ya taya tawagar Najeriya murnar tsallakawa zuwa zagaye na 16 a gasar AFCON 2023.
Kwankwaso ya ce tawagar Super Eagles ta cancanci yabo da kuma kalaman karfafa guiwa, kuma ya yi fatan za su samu nasara a wasannin su na gaba.
Asali: Legit.ng