Kwallon kafa: Jerin kulobs da ka iya biyan kudin da ke kan Lionel Messi

Kwallon kafa: Jerin kulobs da ka iya biyan kudin da ke kan Lionel Messi

A ranar Talata, 25 ga watan Agusta, Lionel Messi ya girgiza Duniyar kwallon kafa, ya shaidawa kungiyar Barcelona cewa ya na so ya tashi.

Rashin jin dadin zaman babban tauraro Lionel Messi ya yi sanadiyyar da ta jawo zanga-zanga da ficewar wasu daga cikin manyan kungiyar Barcelona.

A daidai wannan lokaci ana tunanin zai yi wa Messi mai shekara 33 da haihuwa wahalar komawa kwallo a Nahiyar Amurka ko yankin Larabawa.

Legit.ng Hausa ta tattaro maku jerin kungiyoyin da ake ganin za su iya fansar ‘dan kwallon:

1. Manchester City

Kungiyar Manchester City ta na cikin inda ake tunanin Lionel Messi zai koma idan ya bar Barcelona. Babban dalili kuwa shi ne zai sake haduwa da tsohon kocinsa Pep Guardiola.

Duk da kungiyar ta na da kudi, sai ta yi da gaske na ganin ba ta saba dokar cinikin ‘yan wasa ba.

2. Inter Milan

A Serie A, Inter ce ake tunanin za ta iya fito da makudan kudin da ke kan ‘dan wasan. Fiye da shekara goma kenan da kungiyar ta fara zawarcin Lionel Messi, wannan karo dama ta samu.

Idan Inter ta fito da $800m, za ta rika biyan Messi abin da ya zarce albashin Cristiano Ronaldo.

KU KARANTA: Kocin Barcelona ya na so ya rabu da Suarez, Rakitic, da Vidal

Kwallon kafa: Jerin kulobs da ka iya biyan kudin da ke kan Lionel Messi
Lionel Messi ya ce zai bar Barcelona
Asali: Getty Images

3. PSG

Kungiyar Paris Saint-Germain na cikin wadanda ake ganin za ta iya fansar Lionel Messi. ‘Dan wasan zai samu damar sake haduwa da Neymar Jr., wanda ya bar Barcelona a kakar 2017.

Akwai alamun cewa PSG ta na da kudin da za ta biya wajen sayen wannan ‘dan wasan Duniya.

4. Chelsea

Wata kungiyar Turai da ka iya yunkurin raba Lionel Messi da Barcelona ita ce Chelsea. Kocin kungiyar Ingilar, Frank Lampard ya na sha’awar Messi kamar yadda Rio Ferdinand ya tabbatar.

Matsalar da za a samu ita ce watakila Tauraron ba zai taba kaunar ya bugawa Chelsea wasa ba.

Akwai kungiyoyin hamayya kamar Real Madrid wanda zai yi matukar wahala ciniki ya shiga tsakaninsu da Barcelona. Watakila kuma a iya shawo kan ‘dan kwallon ya zauna a Barcelona

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel