Kwallaye 50 a Cikin Shekarar 2023: Har Yanzu da Sauran Cristiano Ronaldo
- Cristiano Ronaldo ya yi wa masoyansa albishir da cewar yana fatan zura wasu kawallayen kafin karewar shekarar 2023
- Ronaldo ya bayyana hakan ne bayan da ya zura kwallaye 50 a gasar 'kofin sarkin Saudi' wanda ya ba Al Nassr nasar zuwa wasan kusa da na karshe
- Dan wasan gaban ya kasance yana zura akalla kwallo daya a kowanne wasa da ya buga tun bayan ya shiga kungiyar Al Nassr a karshen 2022
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kasar Saudiyya - Dan kwallon duniya, Cristiano Ronaldo ya ce har yanzu da sauran kwallayen da yake fatan zurawa kafin karewar shekarar 2023.
Ronaldo ya bayyana hakan bayan zura kwallonsa ta 50 a kofin 'Sarkin Saudi', a wata fafatawar kungiyarsa ta Al Nassr da Al Shabab, inda wasan ya tashi 5-2.
Tsohon dan wasan gaba na kungiyar Manchester United da Real Madrid ya zura kwallon ne da kafarsa ta dama ana daf da hura tashi wasan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Mun yi nasara kuma ina farin cikin sanar da zura kwallo ta 50 da na yi a wannan shekarar ta 2023,"
A cewar Ronaldo, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Instagram.
Ronaldo ya yi wa mutane albishir
Wannan kwallon da Ronaldo ya zura, ta ba Al Nassr damar zuwa wasan 'na-kusa-da-na-karshe', wanda za a fafata a birnin Riyadh.
Ronaldo ya ce:
"Dukkan godiya ta tabbata ga abokan wasa na, masoyana da kuma iyalina, bisa gudunmowa da goyon bayan da suke nuna mun. Ina fatan sake zura wasu kwallayen kafin shekarar ta kare."
Dan wasan gaban ya kasance yana zura akalla kwallo daya a kowanne wasa da ya buga tun da ya shiga kungiyar Al Nassr a karshen shekarar da ta gabata.
Kano: An nana wa Onana, Yamalash ya magantu kan fashin bakin wasanni da harshen Hausa, ya sha mamaki
A wasannin da kasar Portugal ta buga a shekarar 2023, Ronaldo ya zura kwallaye 10.
Dan wasan Najeriya, Victor Osimhen ya zama gwarzon shekarar 2023
Fitaccen dan kwallon kafa a Najeriya, Victor Osimhen ya lashe gwarzon dan wasan kwallon kafa a Nahiyar Afirka.
Dan wasan ya kafa tarihi inda ya lashe kyautar wanda Nwankwo Kanu ya lashe tun shekarar 1999.
Osimhen ya kara da gwarazan ‘yan wasa kamar su dan kasar Masar, Mohammed Salah da Achraf Hakimi na kasar Morocco
Asali: Legit.ng