Magoya Bayan Juventus Sun Cika Filin Wasa Don Nuna Adawa Da Siyan Lukaku, Sun Ce Ya Tsufa

Magoya Bayan Juventus Sun Cika Filin Wasa Don Nuna Adawa Da Siyan Lukaku, Sun Ce Ya Tsufa

  • Magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Juventus sun nuna kiyayya karara ga Romelu Lukaku yayin da kungiyar ke shirin siyan shi
  • Juventus ta tuntubi kungiyar Chelsea don musanyan Lukaku da Dusan Vlahovic dan shekaru 23 a duniya
  • Magoya bayan tun fara wasan ke ihun kin jinin Lukaku yayin da bayan an tashi daga wasan su ka cika filin wasan don nuna rashin jin dadinsu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Italia – Shirin siyan Romelu Lukaku da kungiyar kwallon kafa ta Juventus ke yi ya samu tasgaro bayan magoyan bayan kungiyar sun nuna ba sa so, Legit.ng ta tattaro.

Kungiyar ta buga wasan sada zumunta a filin wasa na Allianz inda ta yi nasara ta ci kwallo takwas da nema, amma abin da ya fi daukar hankali shi ne yadda magoya bayan su ka nuna kiyayya ga Lukaku.

Kara karanta wannan

Bazoum: 'Gayar Shinkafa' Na Ke Ci Yanzu, Hambararen Shugaban Nijar Ya Koka

Magoya bayan Juve sun nuna damuwa kan siyo Lukaku
Daruruwan Magoya Bayan Juventus Sun Cika Filin Wasa Don Nuna Adawa Da Siyan Lukaku. Hoto: Forza Juve.
Asali: Twitter

Kamar yadda The Guardian ta tattaro, Juventus na shirin musanya da Dusan Vlahovic madadin Lukaku daga Chelsea, amma kungiyar na jan kafa saboda ba su gamsu da Vlahovic ba.

Meye Lukaku ya fuskanta a Juve?

Lukaku ya ki amincewa zuwa kungiyar Inter Milan duk da kungiyar ta daidaita da Chelsea amma ya zabi zuwa abokanan adawarsu wato Juventus.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Forza Juve ta bayyana cewa magoyan bayan kungiyar tun fara wasan su ke ihun cewa ba sa son shirin siyan Lukaku dan kasar Belgium yayin da hukumomin kungiyar ke kara kaimi na siyan shi.

A ina Lukaku ke son buga wasa?

A karshe sun cika filin wasan bayan kamala wasan su na ihu cewa ba sa bukata kuma su na adawa da cinikin saboda za a yi musanya da mai jini a jiki Dusan dan shekara 23.

Kara karanta wannan

Takaddama Ta Kare: Ya Tabbata Messi Ya Fi Ronaldo Wurin Shahara A Kwallon Kafa, Guinness Ya Yi Bayani

Kungiyar Chelsea ta cire sunan Lukaku daga jerin wadanda za su buga mata tambola a bana yayin ya rage masa zabi daya na zuwa Saudiyya da su ka tsuga masa kudi amma Lukaku ya fi son ci gaba da zama a Nahiyar Turai.

Messi Ya Dara Ronaldo A Cin Kofuna Na Guinness

A wani labarin, kamfanin kundin tarihi na Guinness ya fitar da teburin 'yan wasan da su ka fi cin yawan kofuna a kwallon kafa.

Guinness ya fitar da teburin inda ya ke dauke da Lionel Messi a sama da kofuna 41 yayin da Cristiano Ronaldo ke da 40.

Sauran sun hada da Robert Lewandowski da kofuna tara sai Kylian Mbappe da kofuna biyar sai kuma Neymar Junior da guda hudu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.