Yanzu-yanzu: Inter Milan ta karbi aron Victor Moses

Yanzu-yanzu: Inter Milan ta karbi aron Victor Moses

Victor Moses ya saka hannu kan yarjejeniyar buga wa kungiyar Inter Milan kwallo na wucin gadi da zabin su iya sayansa daga hannun Chelsea.

Moses ya tarar da tsohon kocinsa Antonio Conte wanda yanzu shine kocin Inter Milan.

Conte yana amfani da Moses a matsayin wing-back bayan ya canja salon wasan tawagar zuwa 3-4-3 bayan sun sha kaye a hannun Liverpool da Arsenal kamar yadda Sky Sport News ta ruwaito.

DUBA WANNAN: 'Yan ta'addan Boko Haram sun kashe sojoji 8 a Borno

Kocin dan asalin kasar Italiya yana ta farautar 'yan wasa a Premier League da za su dace da irin tsarin wasan kwallonsa inda Moses shine na hudu da ya siyo bayan siyan tsaffin 'yan wasan Machester uku Romelu Lukaku, Alexis Sanchez (wucin gadi) da Ashley Young.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel