Messi Ya Dara Ronaldo Shahara A Kwallon Kafa Bayan Cin Kofuna 41 Da Kundin Bajinta Na Guinness Ya Fitar

Messi Ya Dara Ronaldo Shahara A Kwallon Kafa Bayan Cin Kofuna 41 Da Kundin Bajinta Na Guinness Ya Fitar

  • Lionel Messi ya kara samun fifiko kan abokin hamayyarsa Ronaldo kan cece-kuce da ake kan wanda ya fi shahara
  • Magoya bayan kwallon kafa sun shafe kusan shekaru 20 su na cece-kuce kan wanda ya fi shahara a tsakaninsu
  • Ta tabbata kundin bajinta na Guinness ya kawo karshen wannan cece-kuce bayan fitar da wani teburin kafa tarihi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Miami, Amurka - Kace-nace da ake ta yi kan waye ya fi wani tsakanin shahararrun 'yan wasan kwallon kafa Lionel Messi da Christiano Ronaldo ya zo karshe.

Kundin bajinta na Guinness ya tabbatar da haka bayan fitar da wani rahoto cewa Messi ya dara Ronaldo a cin kofuna a duniya, SportsBrief ta tattaro.

Messi ya dara Ronaldo a yawan kofuna da ya ci a duniya bayan Guinness ya fitar da teburi
Lionel Messi Ya Haura Cristiano Ronaldo Da Kofuna 41 Na Kundin Bajinta Na Kamfanin Guinness. Hoto: @brfootball @AlNassrFC_EN.
Asali: Twitter

Wakilin Legit.ng Hausa ya tattauna da wasu a kan wannan jadawali.

Ali Milan ya bayyana cewa dukkansu zaratan 'yan kwallo amma fa a wurin shi Messi ya fi bajinta.

Kara karanta wannan

Tsohon Abokin Tafiyar Buhari Ya Ambato Kuskuren Da Shugaba Tinubu Ya Fara Daga Hawa Mulki

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce:

"Dukkan su sun yi kokari amma a buga tambola da cin kofuna Messi ya yi gaba.
"Sai dai kuma Ronaldo ya masa fintinkau a zura kwallaye raga."

Shamsuddeen Sani ya ce ai wannan ba wani abu bane don kofi guda daya a tsakaninsu.

Ya ce:

"Idon mu a kan Messi da Ronaldo ba ruwanmu da saura, tafiya za ta yi tafiya kofi daya ba wani abu bane, Ronaldo zai zo ya ba shi ratar goma ma."

Yayin da Abdul Barca ya ce:

"Daga cin kofin duniya kasan Messi ya fi Ronaldo, haka kuma kambun Balon D'or."

Kamfanin Guinness ya kawo karshen cece-kuce

Guinness ya wallafa haka ne a shafinsa na Twitter inda ya ce Messi ya ci kofuna 41 yayin da Ronaldo ke da 40 sai Robert Lewandowski ya zo na uku da kofuna tara.

Kara karanta wannan

“A Raba Aurenmu Dukana Take Yi”: Magidanci Ya Maka Matarsa a Kotu

Shahararrun 'yan kwallon biyu sun sha gwagwarmaya inda su ka shafe shekaru da dama su na gwabza gasa.

'Yan wasan biyu sun ci kyautar Ballon D'or 12 su kadai inda Messi ya ci guda bakwai yayin da Ronaldo ke da biyar, cewar Goal.

Bayan Messi ya ci kofin duniya da aka yi a kasar Qatar, mutane da dama sun tabbatar cewa ya zarta Ronaldo kuma ya kamata ace duk wani cece-kuce ya kare.

Jadawalin yadda Messi ya dara Ronaldo a teburin Guinness

Yayin da wasu ke ganin Ronaldo ya fi shahara a harkan tambola, Messi ya kara samun tabbacin fin kowa bayan kundin bajinta na Guinness ya tabbatar da hakan.

A kundin bajinta na Guinness, Messi na kan teburi da kofuna 41 yayin da Ronaldo ke da 40, Lewandowski shi ne na uku da kofuna tara.

Sannan Kylian Mbappe na kungiyar PSG ya kasance na hudu da kofuna biyar yayin da Neymar Junior ke mataki na biyar da kofuna hudu.

Kara karanta wannan

Mace ta yi Karar Saurayi a Kotu, Ya Yaudare ta Bayan ta Kashe Masa N0.9m a Kano

Messi, Ronaldo Da Sauran 'Yan Kwallo 9 Da Suka Fi Kwazo Cikin Shekaru 10

A wani labarin, Goal ta fitar da jerin gwarazan 'yan kwallo da suka yi fice kuma mafi shahara a kwallon kafa cikin shekaru goma.

Goal ta zabo gwarazan 'yan kwallo 11 da suka hada da Peter Staunton, Stefan Coerts da Sam Brown.

Sun yi zakulo su ne duba da bajintar 'yan wasan a kungiyoyinsu na kwallo daban-daban da kuma kasashensu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.