Cristiano Ronaldo Ya Samu Sabon Kulob, Inda Zai Rika Samun N90bn a Duk Shekara

Cristiano Ronaldo Ya Samu Sabon Kulob, Inda Zai Rika Samun N90bn a Duk Shekara

  • Idan har yarjejeniya ta kammala lafiya kalau, Cristiano Ronaldo zai koma taka leda a kasar Saudi Arabia
  • Bayan ya bugawa kungiyoyin Real Madrid, Manchester United da Juventus, Ronaldo zai tafi Al-Nassr
  • Kudin da za a rika biyan Cristiano Ronaldo a duk shekara zai iya tasan ma miliyan €200m a kungiyar

Qatar - ‘Dan wasan kwallon kafan Duniya, Cristiano Ronaldo zai sa hannu a kwantiragi da kungiyar Al-Nassr nan da ranar 1 ga watan Junairun 2022.

Rahotannin da aka samu daga Marca a kasar Sifen, sun nuna cewa ‘dan kwallon kafan ya samu kungiyar da zai koma bayan tashinsa daga Manchester.

Idan ta tabbata, Ronaldo mai shekara 37 da haihuwazai koma taka leda a Al-Nassr da ke Saudi Arabiya, kuma zai rika karbar tarin albashi mai matukar tsoka.

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda Sun Cukuikuyi Matashin Yana Tuka Ferrari ta Bogi, Zasu Gurfanar Dashi

Ana lissafin cewa kwantiragin ‘dan wasan za ta sa ya rika samun €200m (£172m) a duk shekara, a kudin Najeriya ana maganar kimanin Naira biliyan 93.

Ga albashi ga la'adar Biliyoyi

Rahoton Daily Mail ya nuna idan gaskiya ne, nan da wata guda, tsohon ‘dan wasan na Madrid, Manchester United da Juventus zai rattaba hannu a kwangilar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Abin da kungiyar kasar Saudi Arabiyan za ta rika biyan ‘dan kwallon zai kai kusan £86m, sannan akwai kamasho da zai rika samu daga talla da sauransu.

Cristiano Ronaldo
Cristiano Ronaldo a rigar Al Nassr Hoto: www.marca.com
Asali: UGC

Duk surutun da ake yi ‘dan wasa gaban bai ce uffan ba, ya maida hankalinsa a kan gasar cin kofin Duniya da kasashe suke bugawa a kasar Qatar a halin yanzu.

Tarihin kungiyar Al Nassr

Kungiyar ta saba ganin manyan ‘yan wasan da suka yi wasa a Turai irinsu David Ospina wanda ya yi Arsenal, Luiz Gustavo da irinsu Vincent Aboubakar.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya ce man fetur ba zai iya rike Najeriya, ya fadi mafita ga tattalin arziki

Idan ciniki ya fada, wannan ne karon farko da ‘dan wasan na Portugal zai yi kwallo a wajen nahiyarsa, a baya ya buga wasa a Ingila, Sifen da kasar Italiya.

Punch tace Al-Nassr tana daya cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa da ake da su a Saudi, amma sun yi tsawon shekaru uku rabon da su lashe gasar gida.

Amma a shekarun 2022 da 2021, kungiyar ce ta lashe gasar babban kofin Saudi Super Cup.

Al Nasr ta taba fitowa Duniya a kakar 1999-2000 da ta buga gasar kofin Duniya na kulob, zakarun Turai a shekarar, Real Madrid suka lallasa ta da ci 3-1.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel