Qatar 2022: Yan Kwallon Saudiyya Sun Bada Mamaki, Sun Lallasa Messi Da Ajantina 2-1

Qatar 2022: Yan Kwallon Saudiyya Sun Bada Mamaki, Sun Lallasa Messi Da Ajantina 2-1

  • Yan kwallon kasar Saudi Arabiya sun bada mamaki a ranar Talata a wasar kofin duniya na rukuninsu
  • Saudiyya ta taso daga cin da Lionel Messi yayi mata har ta zura kwallaye biyu a ragar Ajantina
  • Sarkin Saudiyya ya sanar da hutun kwana daya bisa wannan gagarumin nasara da yan kwallonsa suka samu

Qatar - Kasar Ajantina ta sha kashi hannun kasar Saudiyya a wasarsu ta farko a gasar kofin duniya dake gudana yanzu haka a kasar Qatar, daular Larabawa.

Ubangida, Lionel Messi, ne ya bude ragar da fanariti da Ajantina ta samu ana yan mintuna da fara wasar.

Haka aka cigaba da taka leda har zuwa hutun rabin lokaci.

Ana dawowa daga hutun, Ashe Saudiyya ta yi sabon shiri inda Saleh Alsheri ya zura kwallon ramuwa ragar Ajantina a minti na 48.

Kara karanta wannan

Uban 'Yan Sa'a: Wani Mutumi Ya Taki Sa’a, Ya Ci Naira Tiriliyan 1 a Wajen Caca

Bayan mintuna biyar kuwa, Salem Aldwalsari ya zura kwallo ta biyu a minti na 53.

Tsawon wasanni 36 kenan babu wanda ya samu nasara doke Ajantina a duniya, Saudiyya ta kawo karshen wannan abu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Saudi
Qatar 2022: Yan Kwallon Saudiyya Sun Bada Mamaki, Sun Lallasa Messi Da Ajantina 2-1
Asali: AFP

Sarki Salman ya bada hutun kwana 1

Sarkin Saudiyya, Sarki Salman, ya sanar da cewa an bada hutun kwana daya ranar Laraba albarkacin wannan nasara da yan kwallon sukayi kan Ajantina.

A cewar ArabNews, Sarkin ya amince da shawarar da Yarima mai jiran gado kuam Firai Ministan kasar, Mohammed Bin Salman yayi.

An umurci dukkan ma'aikatan gwamnati da masu zaman kansu da dalibai suyi zamansu a gida gobe.

Wasan gaba

Ranar Asabar, yan kwallin Saudiyya zasu kara da kasar Poland, inda Robert Lewandoski ke taka leda.

Yanzu dai Saudiyya ce ke sama a teburin Group C sannan sai Poland da Mexico, sai kuma Ajantina a karshe.

Kara karanta wannan

Lokaci Yayi: Kyawawan Hotunan Kafin aure na Jaruma Halima Atete da Angonta

Ita kuwa Ajantina zata kara da Mexico a wasanta na biyu.

Idan Saudiyya ta samu nasarar doke Poland a ranar Asabar, zata kafa tarihin karon farko na tsallakewa zuwa matakin kifa daya kwala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel