World Cup: Jerin Garuruwa 16 da za ayi amfani da su wajen gasar kofin Duniya a 2026
- Gasar cin kofin wasan kwallon kafa na Duniya na shekarar 2026 zai zo da salon da ba a taba gani ba
- Kasashe uku (Amurka, Kanada da kuma Mexico) suka yi tarayya domin daukar nauyin ‘World Cup’
- Kasashe 48 za su buga wasannin gasar a tsakanin garuruwa 16 tsakanin New York zuwa Toronto
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
United States - Hukumar kwallon kafa ta Duniya watau FIFA ta bada sanarwar kasashen da za a buga wasan cin kofi na Duniya da za ayi a shekarar 2026.
FIFA ta fitar da jerin Biranen da za a biga wannan gasa ne a wani biki da aka shirya a birnin New York.
A shekarar ta 2026, za a buga gasar Duniyan ne a kasashe uku – Amurka, Kanada da Kanada. Bugu da kari, kasashe 48 ne za su fafata a maimakon 32.
A Amurka an zabi Biranen Kansas City, Dallas, Atlanta, Houston, New York/New Jersey, Boston, Seattle, Philadelphia, Miami, San Francisco da Los Angeles
Jaridar ESPN ta ce biranen Mexico da aka zaba domin a buga wasanni a gasar sun hada da Guadalajara, Monterrey, da babban birnin kasar, Mexico City.
Kamar yadda mu ka samu labari, Toronto da Vancouver ne kadai Biranen da aka zaba daga Kanada.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Karon farko a tarihi
Legit.ng Hausa ta fahimci wannan ne karon farko da kasashe uku za su hadu domin dawainiyar gasar cin kofin Duniya wanda ake yi duk bayan shekaru hudu.
A shekarar 2002, kasashen Koriya da Jafan sun yi tarayya wajen shirya wannan gasa. A wancan lokacin Brazil ce ta doke kasar Jamus, ta tafi da kofin zuwa gida.
Idan za a tuna, a 2018 Amurka da makwabanta suka tunkari FIFA domin samun damar daukar nauyin gasar, aka yi dace kasashen suka yi nasara a kan Moroko.
Birane 16 da aka zaba
Ga cikakken jerin Biranen nan kamar haka:
1. Atlanta
2. Boston
3. Dallas
4. Guadalajara
5. Houston
6. Kansas City
7. Los Angeles
8. Mexico City
9. Miami
10. Monterrey
11. New York / New Jersey
12. Philadelphia
13. San Francisco Bay Area
14. Seattle
15. Toronto
16. Vancouver
Asali: Legit.ng