Kungiyar kwallon Lyon ta sallami dan wasa don barka tusa a bainar jama'a

Kungiyar kwallon Lyon ta sallami dan wasa don barka tusa a bainar jama'a

  • Marcelo, dan kasar Brazil ya rasa matsayinsa a kungiyar kwallon Lyon sakamakon laifin tusa bainar jama'a
  • Rahotanni daga faransa sun nuna cewa ya fusata hukumomin kungiyar kwallon ne bayan tusa a dakin shiryawa
  • An tattaro cewa wannan ya biyo bayan kashin da Lyon ta sha 3-0 hannun kungiyar Angers

Kungiyar kwallon Olympique Lynonnais dake kasar taka leda a Ligue 1 a Faransa ta sallami dan wasanta, Marecelo, bayan barka tusa a dakin shiryawan yan kwallo kuma ya fara dariya.

Lyon a watan Agustan da ya gabata cewa an dakatad da dan kwallon kuma an rage masa matsayi bisa dabi'ar da bai dace ba.

A cewar L'Equipe, Marcelo dan shekaru 34 ya barka tusa ne bayan wasa da kungiyar Angers, inda Lyon ta sha kashi kuma Marcelo yaci gida "Own Goal" a wasar.

Kara karanta wannan

'Batanci: Atiku Ya Ce Ba Shine Ya Wallafa Rubutun Sukar Kashe Ɗalibar Sokoto a Shafinsa Ba

An ruwaito cewa bayan fushin da ake da shi bisa cin gidan da yayi, ya barka tusa a dakin 'dressing room' sannan kuma ya fara dariya.

Diraktan harkokin horo na kungiyar, Juninho ya dakatad da Marcelo. Daga baya kuma aka sallamesa a watan Junairu.

Kungiyar kwallon Lyon ta sallami dan wasa don barka tusa a bainar jama'a
Kungiyar kwallon Lyon ta sallami dan wasa don barka tusa a bainar jama'a Hoto: GetFrenchFootball News
Asali: Facebook

Hukumar FIFA da UEFA sun cire Rasha daga cikin duniyar kwallo

A bangare guda, an cire kasar Rasha daga cikin gasar kwallon kofin duniya kuma an dakatad da duka kungiyoyin kwallon kasar daga duniyar kwallo sakamakon yakin da take yi da kasar Ukraniya.

Hukumar kwallon duniya FIFA da hukumar kwallon Turai, UEFA suka sanar da hakan ranar Litinin.

Wannan sanarwa ya shafi dukkan kungiyoyin kwallon dake Rasha irinsu CSKA Moscow, Spartak Moscow, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel