Da duminsa: Hukumar FIFA da UEFA sun cire Rasha daga cikin duniyar kwallo

Da duminsa: Hukumar FIFA da UEFA sun cire Rasha daga cikin duniyar kwallo

  • Bayan yanke Rasha daga manhajar bankuna na SWIFT, duniyar kwallo na kokarin tsame Rasha daga cikin duniya
  • Hukumar kwallon duniya FIFA da hukumar kwallon kasashen Turai da cire Rasha daga harkokinta
  • Kamanin mako guda kenan da Rasha ta fara kutsawa cikin kasar Ukraine

An cire kasar Rasha daga cikin gasar kwallon kofin duniya kuma an dakatad da duka kungiyoyin kwallon kasar daga duniyar kwallo sakamakon yakin da take yi da kasar Ukraniya.

Hukumar kwallon duniya FIFA da hukumar kwallon Turai, UEFA suka sanar da hakan ranar Litinin.

Wannan sanarwa ya shafi dukkan kungiyoyin kwallon dake Rasha irinsu CSKA Moscow, Spartak Moscow, dss.

Da duminsa: Hukumar FIFA da UEFA sun cire Rasha daga cikin duniyar kwallo
Da duminsa: Hukumar FIFA da UEFA sun cire Rasha daga cikin duniyar kwallo

Kara karanta wannan

Mun yi rashin Sojojimu kusan 500, an jikkata kimanin 1600 a Ukraine: Kasar Rasha

A cewar Jawabin hukumomin biyu:

"FIFA da UEFA a yau sun yanke shawarar cewa dukkan yan kwallon Rasha, kungiyoyin kwallo da na kasa, an dakatad da su daga musharaka a wasannin FIFA da UEFA sai baba ta gani."
"Dukkan hukumomin kwallon duniya sun hada kai kan nuna goyon bayansu ga al'ummar kasar Ukraine."
"Shugabannin hukumomin biyu (Gianni Infantino da Aleksander Ceferin) na kyautata zaton cewa lamarin yaki zai yi sauki kuma a dawo zaman lafiya da ake."

Zan Sayar Da Chelsea, Zan Ba Wa Mutanen Da Yaƙi Ya Ritsa Da Su A Ukraine Kuɗin, Abramovich

Mai kungiyar kwallon kafa na Chelsea, Roman Abramovich, a ranar Laraba ya tabbatar da cewa zai sayar da kungiyar ta Firimiya League yayin da Rasha ta kutsa Ukraine, rahoton The Punch.

Biloniyan dan kasar Rasha, Abramovich, ya ce 'zai fi alheri' idan ya rabu da kungiyar da ya sauya ta tun bayan da ya siye ta a shekarar 2003.

Kara karanta wannan

Najeriya ta shiga cikin sahun kasashen duniya 141 da suka bukaci a hukunta Rasha

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Abramovich ya ce:

'Kamar yadda na ce a baya, duk matakan da na ke dauka wadanda za su fi zama alheri ne ga kungiyar."

Asali: Legit.ng

Online view pixel