Ronaldo: Zan Jinkirta Yin Murabus Saboda Ɗana Yana Son Mu Buga Ƙwallo Tare

Ronaldo: Zan Jinkirta Yin Murabus Saboda Ɗana Yana Son Mu Buga Ƙwallo Tare

  • Cristiano Ronaldo, Dan wasan Manchester United da Portugal, ya ce akwai yiwuwar ya jinkirta niyyarsa na yin murabus daga buga kwallo
  • Ronaldo ya ce dansa ya roke shi da ya jinkirta murabus dinsa domin yana son su buga wasan kwallo tare
  • Dan nasa, Cristiano Jr, dan shekaru 11, a halin yanzu yana buga wasa a kungiyar kwallo ta yara na Manchester United

Christiano Ronaldo, dan kwallon kungiyar Manchester United ya ce akwai yiwuwar zai jinkirta yin murabus saboda girmama bukatar da dan sa Cristiano Jr ya gabatar masa, rahoton Vanguard.

Ronaldo, wanda ya cika shekaru 37 a makon da ta gabata ya nuna alamar yana son yin ritaya amma akwai yiwuwar zai jinkarta saboda a yanzu dan sa da ke buga wa kungiyar yara ta United ya roke shi.

Kara karanta wannan

Wani bawan Allah ya daba wa dan Acaba makami har lahira kan ya buge masa Kare a Gombe

Ronaldo: Zan Jinkirta Yin Murabus Saboda Ɗana Yana Son Mu Buga Ƙwallo Tare
Zan Jinkirta Yin Murabus Saboda Ɗana Yana Son Mu Buga Wasa Tare, Ronaldo. Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Ita ma Tribal Football ta rahoto Ronaldo ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Da na ya fada min: Baba, ka sake jira wasu yan shekaru - ina son in buga wasa tare da kai."

Dan wasan, dan asalin kasar Portugal wanda kwantiraginsa a United zai kare a cikin 2023 ya ci kwallo tara a wasanni 23 da ya buga a Premier League da kwallo shida a Champions League a kakan bana.

Ana fatan, Cristiano Jr, mai shekaru 11, zai cike girbin da mahaifinsa zai bari idan ya yi murabus daga kwallon kafa nan ba da dadewa ba.

Bayan Ahmed Musa, Wani Ya Sake Yi Wa Tsohon Dan Wasan Super Eagles Kyautar Naira Miliyan 1

A wani rahoton, Tsohon mai tsaron bayan ya bayyana matsin rayuwa da ya shiga a baya-bayan nan wadda hakan yasa ya fara amfani da motarsa kirar Sienna domin yin kabu-kabu ya ciyar da iyalansa.

Kara karanta wannan

Fasto ya bindige wata mata da ta zo ibada a cocinsa a Ogun

Mr Ujoma, wanda shine shugaban LuckyBay Estate and Properties Limited, ta tabbatarwa Premium Times bada tallafin a safiyar ranar Asabar.

Ya ce ya bada tallafin ne ga Obiekwu saboda ya tausaya masa halin da ya shiga.

Mr Ujomu ya ce:

"Da na ji labarin, na tuntube shi domin sanin sahihancin labarin. Sun aika min da lambar sa (Obiekwu) da lambar asusun bankinsa. Kawai sai na ce bari in tallafa masa da kudin."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel