Fasto ya bindige wata mata da ta zo ibada a cocinsa a Ogun

Fasto ya bindige wata mata da ta zo ibada a cocinsa a Ogun

  • Yan sanda a Jihar Ogun sun kama wani faston cocin Celestial Church of Christ kan zarginsa da yunkurin kisa da mallakar bindiga
  • Faston mai suna Peter Omope ya bindige wata Kemi Johnson ne a kafarta yayin da ta iso cocin cikin dare domin ta yi ibada
  • A halin yanzu an garzaya a Kemi Johson asibiti domin bata kulawa da ta ke bukata yayin da yan sanda suka fara fadada bincike

Jihar Ogun - Yan sandan Jihar Ogun sun kama wani fasto, Peter Omope, kan yunkurin kisa da mallakar makami da aka haramta, rahoton the Punch.

An kama faston mai kula da cocin Celestial Church of Christ, yankin Yesu Yan, da ke Olambe Junction, Akute Jihar Ogun, kan harbin wata bakuwar mai ibada, Kemi Johnson, a kofar shiga cocin.

Kara karanta wannan

Abinda yasa har yanzu dakarun sojin Najeriya ba su ga bayan 'yan bindiga ba, El-Rufai

Kakakin yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.

An kama fasto da ya bindige wata mata a kofar cocinsa cikin dare
Kwamishinan yan sandan Jihar Ogun. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Oyeyemi ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan wani Olalekan ya kira ofishin yan sanda an yi korafi kamar yadda ya zo a rahoton na The Punch.

Oyeyemi ya ce Olalekan ya shaidawa yan sandan cewa shi da Kemi Johnson yar shekara 18 sun kai matar da suke yi wa aiki ne filin tashin jiragen sama ne.

Olalekan ya magantu kan abin da ya faru

Ya ce:

"Bayan mun ajiye madam, mun mayar da motan gidanata kamar yadda ta umurta.
"Amma a hanyarsu na komawa gida sai suka tarar ana wani Ibada na Oro a Olambe don haka ba za su iya bin hanyar ba.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Yan bindiga sun yi garkuwa da jami’in tsaro da wasu mutane a sabon harin Kaduna

"Daga nan suka ga cocin Celestial ana addu'a sai suka ce bari su shiga tunda dai dare ya yi.
"Yayin da suke kofan cocin, wanda ake zargin wanda shine jagoran cocin ya fito da bindiga ya harbi Kemi a kafa kafin su ce masa komai."

An garzaya da yarinyar zuwa asibiti yayin da aka kama faston aka fara bincike.

Kotu ta ɗaure wani matashi da ya yi asubanci ya tafi coci ya sace kujerun roba

A wani rahoton, wata kotun majistare ta daure wani matashi, Lekan Alaka, mai shekaru 19, watanni 3 bisa satar kujerun roba masu kimar N91,200 daga cocin Mount Zion Angelican.

‘Yan sandan sun kama Alaka da laifin sata kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Alkali Olajumoke Somefun ya yanke hukunci bisa tabbatar da laifin da ya aikata bisa ruwayar Vanguard.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel