Buhari: Ka da 'Yan Najeriya su cire tsammani daga Super Eagles
- Shugaba Muhammadu Buhari ya yi martani bayan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya ta sha kashi a hannun yan wasan Tunusiya a ranar Lahadi, 23 ga watan Janairu
- Buhari ya ce jami'ai da yan wasan sun cancanci a jinjina masu duk da cewar basu kai ga tsammanin yan Najeriya ba
- Ya kuma bukaci yan Najeriya da su karfafa masu gwiwa domin su kara himma a gaba
Abuja - Bayan ci daya mai ban haushi da Tunisiya ta yi wa Najeriya a gasar cin kofin Afrika a Garoua, kasar Kamaru, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki yan Najeriya da kada su cire tsammani daga tawagar da jami’anta.
A cewar Buhari, koda dai tawagar basu kai ga tsammanin yan Najeriya ba a gasar, daga jami’ai har yan wasan sun cancanci a yaba masu kan gwagwarmayar da suka yi, rahoton NTA News.
Babban mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin labarai, Garba Shehu, ya bayyana haka a wata sanarwa da ya sanyawa hannu a daren Litinin, 24 ga watan Janairu.
Shugaban kasar ya ce
"Sun baiwa kowa kwarin gwiwar cewa za su iya, kuma na tabbata abu ne da za su iya cimmawa. Duk da haka, bai kamata mu yanke kauna da su ba."
Shugaban kasar ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su kara karfafawa ‘yan wasan guiwa domin su kara himma a karo na gaba, musamman a wasannin share fagen shiga gasar cin kofin duniya da ke gabansu.
Buhari ya umurci hukumomin kwallon kafa na kasar da su yi nazari sosai kan yadda Eagles ta taka leda a gasar cin kofin kasashen.
Hakazalika ya bukaci su karfafawa jama'a gwiwar aikawa hukumar kwallon kafa ta Najeriya da shawarwarin su domin ta duba da kuma shiryawa sosai a gasar cin kofin duniya mai zuwa, rahoton Punch.
AFCON: Kocin Najeriya ya fadi babban dalilin da ya sa Tunisiya ta yi waje da S/Eagles
A gefe guda, mun ji a baya cewa a ranar Lahadi, 23 ga watan Junairu 2020, kocin rikon kwarya na Super Eagles, Augustine Eguavoen ya bayyana dalilin rashin nasarar da suka samu.
Jaridar Punch ta rahoto Augustine Eguavoen yana cewa bai dace kasar Tunisiya tayi waje da Najeriya a zagayen kasashe 16 na gasar cin kofin Afrika na AFCON ba.
An fatattaki ‘yan wasan kwallon kafan Najeriya daga gasar bayan Tunisiya ta doke su da ci 1-0.
Asali: Legit.ng