Taraba
An samu asarar ran mutum ɗaya bayan rufin wani gini ya rufto kan wani gini da ba a kammala aikinsa ba a jami'ar jihar Taraba da ke birnin Jalingo.
Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Taraba ta tabbatar da nasarar gwamna Agbu Kefas na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaɓen gwamnan jihar.
Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya bayyana cewa tsohon gwamna, Darius Ishaku, bai bar masa ko kwandala ba a asusun gwamnatin jihar gabanin miƙa masa mulki.
Rundunar ƴan sandan jihar Taraba ta samu nasarar cafke miyagun ƴan ta'adda masu ɗumbin yawa waɗanda ake zargi da aikata laifin garkuwa da mutane.
Kotun sauraron ƙorafe-korafen zabe mai zama a Jalingo, babban birnin jihar Taraba ta kwace nasarar ɗan majalisar jam'iyyar PDP, ta tabbatar da na APC guda biyu.
Yanzu muka samu labarin yadda kayan abinci suka yi saukar warwas a wasu jihohin Arewacin Najeriya yayin da ake ci gaba da samun tsaiko wajen tsadar kaya.
Manoma sun shiga tsahin hankali a wasu ƙauyuka akalla 15 da ke jihar Taraba biyo bayan ayyukan 'yan bindiga wanda ya tilasta musu hakura da amfanin gonakinsu.
Gwamnatin jihar Taraba karkashin jagorancin Agbu Kefas ta kafa wani kwamiti domin kama duk yaron da ya kamata ace yana makaranta a titi a lokacin makaranta.
Miyagun ƴan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun halaka wata matar aure tare da raunata mijinta a wani sabon hari a jihar Taraba.
Taraba
Samu kari