Taraba: Ishaku Ya Kwashe Komai Baitul Mali Kafin Ya Mika Mun Mulki, Kefas

Taraba: Ishaku Ya Kwashe Komai Baitul Mali Kafin Ya Mika Mun Mulki, Kefas

  • Gwamnan jihar Taraba ya ce ko kwandala bai taras ba a baitul malin gwamnati lokacin da ya karɓi mulki daga Darius Ishaku
  • Mista Agbu Kefas ya ce duk da haka ya tabbata cewa kowane ma'aikaci ya samu haƙƙinsa a kan lokaci a karshen wata
  • Ya kuma sanar da cewa nan bada daɗewa ba gwamnatinsa zata gudanar da bincike don tabbatar da yawan ma'aikata

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Taraba - Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba ya bayyana cewa ya gaji baitul malin gwamnati babu ko kwandala daga magabacin sa, Darius Ishaku, Daily Trust ta rahoto.

Mista Kefas ya faɗi haka ne a ranar Litinin yayin da yake buɗe wani taron karawa juna sani na kwanaki biyar da aka shirya wa sakatarorin ma’aikatu da hukumomi (MDAs).

Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas.
Taraba: Ishaku Ya Kwashe Komai Baitul Mali Kafin Ya Mika Mun Mulki, Kefas Hoto: Governor Agbu Kefas
Asali: Twitter

Gwamna Kefas ya samu wakilcin shugabar hukumar kula da jin daɗin ma'aikata, Misis Suzie Nathan a wurin bikin buɗe taron wanda ya gudana a Jalingo, babban birnin Taraba.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Faɗi Wasu Ƙusoshin Gwamnatin Tinubu Da Suka Fara Tattaunawa Da 'Yan Bindiga

Ya ƙara da cewa duk da ɗumbin kalubalen da gwamnatinsa ta taras jibge, ta ci gaba da biyan ma'aikata albashinsu a kowane ƙarshen wata kuma a kan lokaci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamna Kefas na jam'iyyar PDP ya ce:

"Na gaji baitul malin gwamnati ba bu ko kwandala daga Darius Ishaku, ban samu ko sisi ba a asusun gwamnati da zan fara harkokin shugabanci da su."
"Duk da tulin ƙalubalen rashin kuɗin da na taras, na yi ƙoƙarin tabbatar da cewa kowane ma'akaci ya samu albashinsa a kan lokaci"
"Mun kuma ba da fifiko sosai wajen biyan fansho, sannan kuma mun sanya waɗan da suka aje aiki a tsarin biyan fansho."

Kefas ya sanar da cewa nan ba da daɗewa ba gwamnatinsa zata gudanar da bincike don tabbatar da sahihin yawan ma'aikatan jihar Taraba, kamar yadda Dailypost ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ahaf: Tinubu ya dawo da 'yan Najeriya baya cikin bakin talauci sadda ya cire tallafin mai, malamin jami'a

Ya kuma bada tabbacin cewa nan gaba kaɗan gwamnatinsa zata ɗauki haziƙan matasa aiki yayin da duk ma'aikacin da ya kai matakin ƙara girma za a ɗaga shi.

Gobarar Kotun Koli Ba Ta Kona Takardun Karar Zaben Shugaban Kasa Ba

A wani labarin na daban Kotun ƙolin Najeriya ta bayyana cewa gobarar da ta faru bata shafi ƙarar zaben shugaban ƙasa ba kamar yadda ake yaɗawa.

Mai magana da yawun Ƙotun, Dakta Festus Akande, ya ce kayayyakin da wutar ta cinye za a iya maida su saboda akwai ɗakin karatu na Intanet.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262