Jam'iyyar PDP
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya yi magana kan wanda zai gaje a siyasar 2027. Makinde ya ce wanda zai gaje shi zai iya fitowa cikin jami'ansa da suke tare.
Tsohon Mai Tsawatarwa a Majalisar Dattawa, Sanata Agboola Ayoola ya mika wasikar ficewarsa daga jam'iyyar PDP a jihar Oyo, ya ce zai canza akalar siyasa.
Mai taimakawa tsohon gwamnan Benue, Gabriel Suswam, ya karyata jita-jitar cewa ya koma APC, yana cewa gayyatar Gwamna Alia ba ta da nasaba da siyasa.
Kwamitin rikon kwarya da APC ta kafa a jihar Enugu ya tabbatar da cewa Gwamna Peter Mbah da mukarrabansa za su dawo jam'iyya mai mulkin Najeriya a makon gobe.
Tsohon minista a Najeriya, Farfesa Isa Ali Pantami ya gana da shugaban jam'iyyar PDP mai adawa, Ambasada Umar Iliya Damagum tare da tawagarsa a Abuja.
Kungiya a Arewacin Najeriya da ke goyon bayan jam'iyyar PDP ta ce babu ja da baya kan marawa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan baya a zaben 2027
A labarin nan, za a ji cewa rikicin jam'iyyar adawa ta PDP ta kara fada wa a cikin rikici, lamarin da ya jawo ta dakatar da sakatarenta saboda wasu zarge-zarge.
Babban jigon APC a yankim Kudu maso Gabas, Mista Onoh ya celokaci ya yi da jam'iyyar za ta hada kai a jihar Enugu karkashin jagorancin Gwamna Peter Mbah.
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya taso jam'iyyun adawa a gaba. Ya nuna cewa jam'iyyun suna cikin wani hali saboda rikice-rikicen da suka mamaye su.
Jam'iyyar PDP
Samu kari