Jihar Ondo
IGP Kayode Egbetokun ya sanar da tura jami'ai 22,239 zuwa Ondo don tabbatar da tsaro a zaben gwamna mai zuwa. Ya kuma zargi jam'iyyun siyasa da haddasa husuma.
Babbar Kotun jihar Ondo ta yi fatali da korafin masu kalubalantar takarar Olugbenga Edema a zaben gwamnan Ondo kan zargin cewa ba dan NNPP ba ne.
Dan takarar jam'iyyar NNPP a zaben jihar Ondo, Gbenga Edema yana cigaba da jiran tsammani duk da daura kwanaki 11 a gudanar da zabe duba da korafi da ke kansa.
Yayin da ya rage ƴan kwanaki a fita zaɓen gwamna a jihar Ondo, tsohon ɗan majalisar tarayya da wasu manyan ƙusoshin PDP sun haɗe da Gwamna Aiyedatiwa a APC.
Yayin da ake shirye-shiryen zabe a jihar Ondo, Gwamna Aiyedatiwa kuma ɗaɓ takarar APC ya ce zai fara biyan sabon mafi karancin albashi na N73,000 a Nuwamba.
Shugaban malaman addinin Musulunci a jihar Ondo ya goyi bayan dan takarar gwamnan APC a zaɓen Ondo. Malaman Musulunci sun ce za su zabi APC a Ondo.
Babban sarki a jihar Ondo, Oba Olufaderin Adetimehin ya goyi bayan dan takarar gwamnan APC a zaɓen gwamnan Ondo da za a yi a shekarar 2024 da muke ciki.
Mataimakiyar dan takarar gwamna a jam'iyyar SDP a jihar Ondo, Susan Gbemisola Alabi ta watsar da jam'iyyarta inda ta dawo APC mai mulkin Najeriya.
Mutane da dama sun gudanar da zanga-zanga a hedkwatar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ke birnin tarayya Abuja a ranar Talata, 29 ga Oktoba 2024
Jihar Ondo
Samu kari