Ogun
Rahotanni sun tabbatar da rasuwar mataimakiyar mai tsawatarwa a Majalisar Wakilai, Hon. Adewinmi Onanuga wacce ta rasu a yau Laraba 15 ga watan Janairun 2025.
Wasu ɗalibai sun farmaki ayarin mataimakiyar gwamnan jihar Ogun, Noimot Salako-Oyedele yayin da ta fito za ta je taron tunawa da jami'an sojoji na bana.
Yayin da yunwa ta addabi al'umma a Najeriya, dan majalisar wakilai, Gboyega Nasir Isiaka, ya ba da shawarar amfani da fasahohin zamani da na gargajiya a noma.
Ana cikin jimami da mahaifiyar tsohon shugaban majalisar wakilai, Dimeji Bankole, ta yi bankwana da duniya bayan fama da rashin lafiya mai tsawo.
Rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta kama wasu matasa da ake zargi da satar wayar wuta da karafuna a gidaje suna sayarwa 'yan bola jari. Za a gurfanar da su a kotu.
Hukumar ƴan sandan jihar Ogun ta tabbatar da mutuwar wani jami'in tsaro mai zaman kansa bayan ya yanke jiki ya faɗi a bakin aiki, an fara gudanar da bincike.
Tsohon dan takarar shugaban kasa a NNPP, Sanata Kwankwaso ya kai ziyara ta musamman har gidan tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo a Abeokuta.
Wasu matasa da ake kyautata zaton 'yan dabar siyasa ne sun yi awon gaba da sandar majalisar karamar hukumar Abeokuta ta Arewa a jihar Ogun ana tsaka da rantsuwa,
Majalisar dokokin jihar Ogun ta bukaci shugabannin kamfanin Dangote da su bayyana gabanta domin amsa tambayoyi kan ayyukan kamfanin a yankin Ibese.
Ogun
Samu kari