Ministar Tinubu Ta Bayyana Malamin Addinin da Ya Mata Addu’a Ta Samu Mukami, Ta Yi Godiya

Ministar Tinubu Ta Bayyana Malamin Addinin da Ya Mata Addu’a Ta Samu Mukami, Ta Yi Godiya

  • Dakta Betta Edu, Ministar jin kai da walwala ta bayyana silar samun mukamin Ministarta a gwamnatin Tinubu
  • Betta ta ce Fasto David Oyedepo shi ne silar samun mukamin nata saboda addu’ar da ya mata a 2022
  • Ministar ta ce a taron na shekarar 2022 ta roki Faston ya mata addu’a ta dawo a 2023 a matsayin Minista

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Ministar jin kai da walwala, Dakta Betta Edu ta bayyana yadda aka yi ta samu mukamin Minista a gwamnatin Shugaba Tinubu.

Edu ta ce ta samu mukamin ne bayan Fasto David Oyedepo ya yi mata addu’a a yayin wani taro a cocinsa, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Gagaruman abubuwa 3 da za su faru a 2024, malamin addini ya yi hasashe

Edu ta fadu malamin addinin da ya mata addu'a ta samu mukamin Minista
Betta Edu ta yi godiya ga Faston da ya mata addu'a ta samu Minista. Hoto: Bola Tinubu, Betta Edu.
Asali: Facebook

Mene dalilin samun mukamin Minista Edu?

Ministar ta ce hakan ya faru a babban taron ‘Shilo’ a 2022 a farkon makon watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Shiloh’ taro ne da ake yi ko wace shekara da ya ke daukar hankalin miliyoyin Kiristoci a fadin Najeriya.

Ta ce Fasto David Oyedepo shi ya yi mata addu’a a yayin taron wanda ta samu halarta inda ya yi sanadin samun wannan mukami nata.

Wane martani Edu ta yi?

Ta ce:

“A bara yayin taron ‘Shiloh’ na 2022, na yi addu’a inda na roki ubangiji cewa zuwa wata shekara da zan zo ‘Shiloh’ ina son zama Ministar Najeriya.
“A ranar karshe ina shirin fita sai na ci karo da Baba Oyedepo sai na fada masa cewa ina son ya mini addu’a.
“Ya tambaye ni abin da na ke bukata, na ce masa ina son na dawo ‘Shiloh’ wata shekara a matsayin Ministar Tarayyar Najeriya, inda ya dora hannunsa a kai na ya min addu’a.”

Kara karanta wannan

Kaduna: Gwamna Sani ya caccaki kalaman DHQ kan dalilin jefa bam a taron Musulmai, ya nemi abu 1

Edu ta godewa ubangiji inda ta ce gashi yanzu ta dawo a matsayin Minista a Najeriya inda ta ce ta na daga cikin masu kananan shekaru, cewar Vanguard.

Edu ta fadi lokacin biyan basukan N-Power

Awani labarin, Ministar jin kai da walwala, Betta Edu ta yi alkawarin biyan basukan N-Power a watan Janairu.

Edu ta ce su na ci gaba da kwaskwarima ne ga shirin saboda matsalolin da ke ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel