Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Sahihancin Nasarar Shugaban Majalisar Dokokin Jihar APC

Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Sahihancin Nasarar Shugaban Majalisar Dokokin Jihar APC

  • Kotun ɗaukaka kara mai zama a Abuja ta raba gardama kan kujerar shugaban majalisar dokokin jihar Ogun, Olakunle Oluomo
  • Da take yanke hukunci, kotun ta tabbatar da nasarar kakakin majalisar kuma ta ci tarar ɗan takarar PDP wanda ya shigar da ƙara
  • Bayan haka kuma majalisar dokokin Ogun ta rantsar da sabon mamba mai wakiltar mazaɓar Ikenne a inuwar APC

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a babban birnin tarayya Abuja ta yanke hukunci kan shari'ar da aka kalubalanci nasarar kakakin majalisar dokokin jihar Ogun.

A zaman yanke hukunci ranar Talata, kotun ta tabbatar da nasarar kakakin majalisar, Honorabul Olakunle Oluomo, a zaɓen mazaɓar Ifo 1 ta jihar Ogun.

Kara karanta wannan

Wike vs Fubara: Jerin yan siyasan da suka sanya hannu a yarjejeniya kawo karshen rikicin Rivers

Kotun ɗaukaka kara ta yanke hukunci.
Kotun daukaka kara ta yanke hukunci kan sahihancin nasarar shugaban majalisar dokokin jihar APC Hoto: Court of appeal
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, ɗan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a mazaɓar, Okikiola Ogundele, shi ne ya ƙalubalanci nasarar Oluomo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun da farko, kakakin majalisar Ogun ya samu nasara a kotun sauraron ƙorafe-korafen zabe, amma ɗan takarar PDP ya sake kalubalantar hukuncin a kotun ɗaukaka ƙara.

Kotun daukaka kara yayin da take tabbatar da nasarar Oluomo ta kuma ci tarar N500,000 ga wanda ya shigar da kara.

Kakakin majalisar ya yi martani kan hukuncin

Da yake tsokaci kan hukuncin da kotun ɗaukaka kara da yanke, Oluomo, ya ce hakan ya ƙara tabbatar da nasarar da ya samu tun farko a zaben 18 ga watan Maris.

A cewarsa, bisa haka ne ya ke ta samun nasara tun daga lokacin kaɗa kuri'u a akwatunan zaɓe har zuwa kotun ɗaukaka ƙara.

Kara karanta wannan

Kotun Daukaka Kara ta raba gardama, ta yanke hukunci kan nasarar Tambuwal da Wamakko

An rantsar da sabon mamba a majalisar Ogun

Bayan haka kuma majalisar dokokin jihar Ogun ta rantsar da Olakunle Sobukanla a matsayin sabon ɗan majalisa mai wakiltar Ikenne a inuwar jam'iyyar APC.

Kakakin majalisar, Olakunle Oluomo, ne ya jagoranci rantsar da sabon mamban majalisar yayin zaman ranar Talata, kamar yadda PM News ta ruwaito.

Zamu hukunta Wike da wasu jiga-jigai - Damagum

A wani rahoton na daban Shugaban PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana cewa Wike zai gane bai fi karfin jam'iyya ba a lokacin da ya dace.

A cewarsa, ba tsohon gwamnan jihar Ribas ne kaɗai ya ci amanar PDP a babban zaben 2023 ba, akwai wasu kuma duk za a hukunta su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel