Hukumar Sojin Najeriya
Wata babbarkotun tarayya mai zama a Abuja ta amince da bukatar hukumar leƙen asiri ta ƙasa DIA ta tsare mutum 20 da ake zargi da hannu a al'amuran ta'adanci.
A ci gaba da lallashin ƙasashen Nijar Mali da Burkina Faso, babban hafsan tsaron Najeriya Janar Christopher Musa ya kai ziyara ga takawaransa na Nijar.
Shugaban rundunar sojojin ƙasan Najeriya, Laftanar Janar Lagbaja ya ce ko alama sojoji ba za su kawar da gwamnatin demomuraɗiyya a ƙasar nan ba .
Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa jami'an tsaro sun yi nasarar ceto ɗalibai 20 da aka yi garkuwa da su a hanyar zuwa wurin taro kusan mako guda da ya. gabata.
Hedkwatar tsaron Najeriya ta bayyana cewa dakarun sojoji sun yi nasarar kashe ƴan ta'adda 171, sun kamo miyagu 302 a mako guda da ya gabata a sassan Najeriya.
Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya yi Allah wadai da kisan Sarkin Gobir hakimin Gatawa, Isah Bawa, ya ce ba zai yiwu makasan basaraken su ci bulus ba.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar fatattakar ƴan bindiga a yankin ƙaramar hukumar Wase da ke jihar Filato, sun kashe akalla 15daga cikinsu.
Sheikh Abdulrahaman Azzamfari ya nuna damuwa kan halin rashin tsaron da al'umma suka tsinci kansu a jihar Zamfara sakamakon hare-haren ƴan fashin daji.
Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bijiro da wata manhaja mai suna mobilizer da za ta ba wa yan kasa damar mika sakon ta'addanci ko rashin tsaro a yankunansu.
Hukumar Sojin Najeriya
Samu kari